Sabon rikicin da ya kunno kai a Jami’yyar APC tun bayan kammala zaben fid da gwani da aka gudanar, na neman zama wata sabuwar hanyar da ka iya kai jamiyyar rijiya gaba dubu (wanda ya fada ya tafi kenan).
Yanzu haka dai masana na ci gaba da yin sharhi a kan wannan matsala da take neman raba jamiyyar APC gida biyu a Jihar Katsina bayan musayar kalamai da ke tada kura daga bangarori biyu.
Mukadashin shugaban tsangayar siyasa a Jami’ar Umaru Musa Yar’adua da ke Katsina, Dakta Kabir Musa Yandaki ya jaddada cewa matukar ba a dauki mataki cikin sauri ba, makomar APC a Katsina shi ne tana iya dafa kasa ko ma ta zubar da ciki wato dai faduwar zaben da za a yi.
Ya kara da cewa ita jami’yyar a irin wannan lokaci babu abin da take bukata kamar dinke duk wata baraka da rikicin cikin gida, domin fuskantar zabe da sauran jam’iyyun siyasa da ke dakun karawa da ita.
“Maganar da mataimakin shugaban jam’iyyar APC na Jihar Katsina, Bala Abubakar Musawa ya yi, magana ce mai tsadar gaske a irin wannan lokaci da ake neman jama’a ba wai a kore su ba kamar yadda ya yi barazana,” in ji shi.
Bala Abu Musawa dai an ruwaito shi a gaban Gwamna Aminu Bello Masari a karamar hukumar Malumfashi inda suka je bude wasu ayyuka, ya furta cewa ko APC za ta fadi zabe sai sun hukunta wadanda suke halartar wasu tarurruka da suka yi zargin ana cin mutuncin Buhari da Gwamna Masari.
Tun kafin Bala ya yi wannan martani, tsohon sakataran gwamnatin Jihar Katsina kuma daya daga cikin wadanda suka nemi takarar gwamnan jihar bai samu nasara ba, Dakta Mustapha Inuwa ya yi wani taro da kungiyoyi da magoya bayansa, inda ya yi wasu maganganu da ake ganin ya kasa nuna juriya a siyasa.
Daga cikin maganganun da Dakta Mustapha Inuwa ya yi ya ce, an ci amanarsa, sai dai kai-tsaye bai kira sunan wanda ya ci amanarsa ba, amma dai masu sharhi siyasa na ganin wannan magana tasa da Gwamna Aminu Bello yake yi.
Sannan Dakta Mustapha ya kara da cewa duk wani magoyin bayansa da aka yi wa ba daidai ba a cikin jamiyyar APC, to duk inda ya koma zai taimaka masa, batun da ake ganin kamar ya shirya yi wa jam’iyyar APC zagon kasa.
Duk da irin zafin da Dakta Mustapha Inuwa ya dauka sai da ya kara jaddada cewa ya karbi wannan sakamakon a matsayin kaddararsa, sai dai a cewarsa hakan ba yana nufin idan an yi maka ba daidai ba ko magoya bayanka, kuma a ce ba za su yi magana ba.
Babu shakka, ba wanda yake ja da cewa Dakta Mustapha Inuwa bai san tsari da kuma yadda ake tafiyar da siyasar Katsina ba, ya fada da bakinsa wanda ake ganin maganar a matsayin gori, inda ya ce gwamna bai san yadda ake cin zabe ba, sai dai a kawo masa sakamakon zaben an cinye duka.
Sannan ya kara jefa wani kalubale kamar yadda ya saba fada a wasu tarurruka cewa tun da aka ba shi mukamin Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina na tsawan shekara bakwai ya rike amana ba a taba hada baki da shi aka yi rashin gaskiya ba, idan kuma an yi bai yafe wa duk wanda ya rufa masa asiri ba.
A wani bangare na maganganun da suka harzuka Bala Abu har ya yi wancan martani, akwai wasu kalamai da daya daga cikin dakurun gwagwarmayar neman takarar Mustapha Inuwa, tsohon shugaban jam’iyyar APC kuma sakatare a yanzu Malam Shitu Maslaha ya yi.
A cikin jawabin da ya yi a wajan wannan taron, ya yi takaicin yadda masu zaban fid da gwani suka ki zaban dan takararsa, inda a karshe ya ce kashi 70 daga cikinsu (daligetet) jahilai ne.
Malam Shitu Maslaha ya ci gaba da cewa daman ya ji tsoron ka da wannan tafiya ta su ta yi irin karkon siyasar Buhari, wato ya fara da farin jini amma zai kare da zagi, wadannan kalamai da Dakta Mustapha Inuwa da Shitu Maslaha su ne musababin wancan magana ta Bala Abu Musawa.
Tun da farko kafin Shitu Maslaha ya fara jawabi, ya yi bayanin cewa ya mika ne a wannan wuri a matsayinsa na dan gwagwarmayar neman takarar Dakta Mustapha Inuwa ba a matsayinsa na sakataren jam’iyar APC na Jihar Katsina ba.
Saboda haka ya ci gaba da baro bayanai masu kama da zazzage abin da ke cikinsa na yadda suka ji bayan kammala zaben fid da gwani wanda ya zargi Gwamna Aminu Bello Masari kan ya mara wa Dikko Umar Radda baya.
Hakikka daga jin yadda Shitu Maslaha ke magana ka san ya sha ta dubu, wato dai komi zai faru sai dai ya faru, har tarihin siyasarsa ya bayar da irin tsawon lokacin da ya dauka yana adawa, kuma kamar ya shirya fara wata sabuwar adawar tun da maigidansa ya rasa takara.
Wadannan maganganu sun jefa masana da manazarta masu sharhi a kan harkokin siyasa jihar, sabon nazari da karatun ta nutsu a bangaren siyasar Jihar Katsina da kuma makomar ta a zaben 2023.
Kamar yadda Dakta Kabir Musa Yandaki ya fada cewa, ita jami’yya tana da tsarin da take bi wajan hukunta ‘ya’yanta idan sun yi ba daidai ba, amma maganar cewa ko za a fadi zabe sai an hukunta masu halartar irin wancan taro ba daidai ba ne a siyasa.
Ya kuma kara da cewa wannan rikicin cikin gida ne wanda ya kamata a ce Gwamna Aminu Bello Masari ya yi wa tufkar hanci tun kafin abin ya yi nisa, inda ya ce idan aka ci gaba da wannan rikicin cikin gida, to karshe magana shi ne faduwa zabe za a yi ba tare da wata tantanma ba.
A cewar Dakta Kabir Musa Yandaki, su sauran jam’iyyu wannan fadan yana yi masu dadi kuma ba sa so ya kare, domin idan aka ci gaba su za su amfan ta hanyar yi wa jam’iyyar APC dukan kawo wuka a zaben 2023.
Idan ba a manta ba, lokacin da ake tafka shari’a tsakanin Gwamna Aminu Masari da Lado Danmarke, Bala Abu ya yi irin wannan barazanar inda ya ce za su sa mace ta kori duk wanda suka samu da hannu wajan taimaka wa su Lado a kan batun shari’ar da ake yi da su, amma dai haka maganar ta wuce kamar bikin Sallah.
Babban abin da ya fi ba wasu mamaki a cikin maganganun Bala Abu shi ne, za a kori duk wanda ya kara halartar wani taro da ake cin mutuncin Buhari da Gwamna Masari, amma bai ce za a kori mai shirya taron ba, tun da an ce za a ci gaba da yin taron daga lokaci zuwa lokaci.
Wannan musayar yawo dai ta haifar da muhawara sosai a kafafen yada labarai na zamani (Social Media), inda wasu daga cikin masu kaunar Gwamna Masari suke kallon wadancan kalamai tamkar raini ne ga shugaba inda har suka fara mai da martani.
Haka a bangaren tsohon sakataran gwamnatin Jihar Katsina su ma sun fara yada bakaken maganganu da ake ganin rashin dacewar su a siyasa. Matukar jam’iyyar APC dai ba ta son barin ciki a zaben 2023 a Jihar Katsina, ya zama wajibi ta lalubo yadda za ta magance wannan matsalar.