Bayan kammala zabukan fitar da gwanaye na jam’iyyun siyasa musamman APC da ke mulki a Nijeriya da kuma PDP da ta yunkura take son kwace mulki a yayin babban zaben 2023 da ke tafe.
Wanda hakan ya tabbatar da Asiwaju Bola Ahmad Tinubu daga yankin Kudu a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC da kuma Atiku Abubakar daga Arewa Maso Gabas a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, sai kuma kallo ya karkata zuwa kan su waye za su zaba a matsayin mataimaka.
Kazalika, sauran jam’iyyun irinsu NNPP ta tsayar da tsohon gwamnan jihar Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso ne a matsayin dan takararta.
Wakilinmu ya labarto cewa manyan jam’iyyu biyun sun sha kwaranniya kan yadda za su zabi mataimaka, lamarin da ya sanya ‘yan takaran suka shiga tsaka mai wuya na neman mataimaka musamman ma a jam’iyyar APC.
A bisa lura da yadda siyasar kasar nan ke tafiya, ana duba shugaba daga wani yanki ya fito kana a zabi mataimaki daga wata yanki domin tabbatar da tafiya da kowani yanki cikin sha’anin mulki da shugabanci.
A jam’iyyar APC dai Bola Ahmad Tinubu ya fito karara ya nuna cewa iko da dammar zabar mataimakin shugaban kasa na hannunsa ne, kan hakan ne ake kyautata zaton zai dauki dan arewa maso gabas kuma kirista. Kodayake ya sha kusa dangane da tunanin da wasu ke yi na cewa zai iya zabar musulmi kuma daga yankin arewa a matsayin mataimakinsa.
Domin neman hadin kai da cigaban jam’iyyar, masu ruwa da tsaki na APC sun yi tir da matakin daukan musulmi a matsayin mataimaki lura da cewa Bola Tinubu musulmi ne da ya zama dan takara, sun dan nace kan cewa dole ne Tinubu ya dauki kirista kuma daga yankin arewa.
A dai yau Juma’a 17 ga watan June wa’adin da hukumar zabe ta bai wa jam’iyyu na su gabatar mata da sunayen ‘yan takata da mataimakansu. Kan hakan ne suka bazama neman mataimaka.
A wata hira da aka yi da gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodinma, ya bayyana cewar damar zabar mataimakin shugaban kasa na hannun Tinubu ne. Ya ce, babu inda aka bayyana cikin kundin tsarin mulkin kasa cewa dole ne sai Musulmi ya dauki kirista a matsayin mataimakinsa, ya ce kawai sai ana yin hakan ne domin cigaba da kuma hadin kai a tsakanin yankunan kasar nan.
Bisa kin amincewa da wasu masu ruwa da tsaki suka yi na tikitin Musulmi da Musulmi, hakan ta sanya ake kyautata zaton Tinubu zai iya daukar tsohon Kakakin Majalisar tarayya, Honorable Yakubu Dogara a matsayin mataimakinsa.
Dogara dai kirista ne kuma ya fito ne daga yankin Arewa Maso Gabas, don haka ne ake harsashen zai iya samun wannan damar.
Kodayake bayan Dogara, akwai wasu da ake ganin Tinubu zai iya zaba kamar su Simon Lalong na jihar Filato da Nasir El-Rufa’i na Kaduna da kuma Muhammad Badaru Abubakar na Jigawa. Da kuma gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum, da kuma tsohon gwamnan Benue George Akume. Amma harsashe ya fi karfi kan Dogara dan asalin jihar Bauchi.
Kodayake daga fari Gwamnonin APC Sun so zabar wa Tinubu mataimaki, amma hakan bai samu ba, inda alamu suka nuna Tinubu da jam’iyyar APC za su yi gaban kansu ne su dubi wanda suke ganin zai iya kawo musu kuri’a da za su iya cin zabe ba tare da duba addini ko bangaren da ya fito ba.
A bangaren jam’iyyar PDP kuwa, ana kyautat zaton cewa Atiku Abubakar zai zabi gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike ne a matsayin mataimakinsa da za su yi takarar 2023 a tare.
Ana tunanin Atiku Abubakar zai zabi Wike ne domin cike kibin siyasa da kuma kasancewarsa dan yankin Kudu, lura da cewa shi Atiku ya fito daga yankin Arewa.
Wike dai ya fito neman tikitin Shugaban kasa a jam’iyyar PDP inda Atikun ya kayar da shi da kuri’u 371 yayin da shi kuma Wike din ya samu kuri’u 237 a zaben fitar da gwani da suka gudanar kwanakin baya a Abuja.
Bayan Wike akwai rade-radin cewa jam’iyyar da dan takararta Atiku Abubakar na shirin daukar tsohon gwamnan Imo Emeka Ihedioha.
Kazalika NNPP da ta tsayar da Rabi’u Musa Kwankwaso akwai yiwuwar ta dauko nata mataimakin daga Kudanci.