Gwamnatin Tarayya ta tsoma baki cikin rikicin da ke faruwa tsakanin Aliko Dangote da hukumar kula da Man Fetur ta ƙasa (NMDPRA) game da batutuwan da suka shafi aikin matatar Dangote a Legas.
Dangote ya bayyana damuwarsa game da matsalolin shigo da ɗanyen mai, yana danganta ƙalubale da cikas da wasu masu hannu da shuni ke kitsa wa don taɗile nasarar matatar.
- Na Fi Fifita Kishin Ƙasa A Kan Tara Riba – Dangote
- Abokan Kasuwancinmu Na Zuwa Akai-akai Don Neman Kayayyakin Da Mu Ke Tacewa- Dangote
Matsalar dai ta ƙara tsananta ne lokacin da NMDPRA ta bayyana cewa matatar ba a ba ta lasisin fara aiki ba tukuna, inda Shugaban hukumar, Farouk Ahmed, ya ce matatar tana cikin matakin kafin fara aiki, kuma man dizal ɗin da take samarwa bai kai ma’aunin duniya ba—wanda Dangote ya karyata ƙarya ta wannan iƙirari.
Kan wannan batu, Ministan Albarkatun Man Fetur, Sanata Heineken Lokpobiri, ya shirya babban taro tare da masu ruwa da tsaki, ciki har da Aliko Dangote, Farouk Ahmed, Gbenga Komolafe na hukumar kula da NUPRC, da Mele Kyari na Kamfanin Man Fetur na ƙasa (NNPC). Taron ya na nufi magance matsalolin da ke neman dabaibaye matatar Dangote.
Mahalarta taron sun nuna godiya ga jagorancin ministan da kuma jajircewarsa wajen yunƙurin nemo mafita mai ɗorewa ta hanyar haɗin gwuiwa.