An ce an kashe mutane biyu a wani rikicin fili da ya barke tsakanin kabilar Kambari da Fulani a garin Salka da ke karamar hukumar Magama a Jihar Neja.
Wannan lamari ya kai ga kone ofishin ‘yansanda, da fadar shugaban yankin da kuma wasu bukkokin Fulani akalla guda 30.
- Gwamnati Ta Kama Mutum 80 Da Zargin Taimakawa ‘Yan Bindiga A Jihar Zamfara
- Babu Cutar Da Ta Barke A Sansanin ‘Yan Gudun Hijiranmu – Gwamnatin Kogi
An tattaro cewa lamarin ya faru ne a ranar Litinin.
Wani ganau ya ce rikicin ya fara biyo bayan cece-kuce kan mallakar wani fili da ake zargin wani Bafulatani ya raunata wani dan kabilar Kambari da gatari.
Majiyar ta bayyana cewa a sakamakon haka ne fada ya barke tsakanin bangarorin biyu wanda ya yi sanadin mutuwar mutane biyu.
Wakilinmu ya tattaro cewa filin da ake magana ya zama abin cece-kuce.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Sakataren gwamnatin jihar, SSG, Alhaji Ahmed Ibrahim Matane, ya koka da yadda lamarin ya faru, inda ya ce an baza jami’an tsaro a yankin domin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Har ila yau, da aka tuntubi kwamishinan tsaro na cikin gida da ayyukan jin kai, Emmanuel Umar, ya ce gwamnatin jihar tana kan gaba wajen ganin an dawo da zaman lafiya a yankin.