Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya tafi Turai kan harkokin kasuwanci.
Mista Paul Ibe, mai bai wa Atiku shawara kan harkokin yada labarai ne, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata a Abuja.
- Atiku Ya Yi Alkawarin Dawo Da Zaman Lafiya Da Sake Farfado Da Masana’antu A Jihar Kaduna
- Matsalar Da Amare Ke Fuskanta Ta Rashin Dorewar Soyayyar Ango
Ibe ya ce tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi balaguro ne a daren Litinin din da ta gabata don ganawa da abokan sana’o’in kasuwanci na daya daga cikin wadanda annkbar COVID-19 ya shafa da kuma koma bayan tattalin arziki.
Talla
Ibe ya ce taron zai kuma mai da hankali kan shawarwarin gamayyar kungiyoyi don fadada ayyukan da aka yi niyya.
Talla