Kasashen duniya na ci gaba da tofin Allah-tsine kan harin da ya janyo kisan daruruwan fararen hula a wani asibitin Gaza da ake zargin isra’ila da kaiwa.
Duk kokarin da kasashen duniya ke yi na ganin an samu maslaha kan rikicin Gaza, da alama abin ya ci tura sakamakon yadda ake dada samun rarrabuwar kawuna tsakanin masu tausayin Falasdinawa da magoya bayan Yahudun Isra’ila.
- Zaman Lafiya: MDD Ta Fara Yunkurin Samar Da Wani Sabon Tsari A Kaduna Da Katsina
- Sin Ta Kafa Kyakkyawan Misali A Fannin Kare Hakkokin Bil Adama
A wannan makon, an soke ganawar Shugaban Amurka Joe Biden da wasu shugabanni na Kungiyar Hadin Kan Larabawa a kasar Jordan.
Wakazalika, kasashen duniya masu tausayin Falasdinawa sun mara baya ga wani kudiri na tsagaita wuta da kasar Brazil ta gabatar wa zauren Majalizar Dinkin Duniya, sai dai Amurka ta hau kujerar na-ki a kan tabbatar da aiki da kudirin bisa abin da ta ce “ba a yi wa Isra’ila adalci ba a ciki”.
Kasashen Asiya sun yi hannun riga da na Turai kan yakin da ake yi a Zirin Gaza.
…Masar Ta Bude Kan Iyakarta Da Gaza Domin Kai Taimako
Rahotanni daga kafofin yada labarai sun bayyana cewa Masar ta bude iyakarta da Gaza na wani dan lokaci domin bari a shigar da kayan agaji da kuma kyale ‘yan kasashen waje su fita.
Sai dai Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ba ta tabbatar da rahotannin ba.
Wani sako da aka wallafa a shafin sada zumunta, ya bai wa Amurkawa da ke Gaza shawarar cewa su matsa kusa da iyakar Rafah idan suka tabbatar babu wani hadari.
A ranar Laraba ne Shugaban Amurka ya kai ziyara Isra’ila a karon farko tun bayan harin da Hamas ta kai a ranar 7 ga wannan watan.
…Harin Asibitin Gaza: Shugaban Amurka Ya Wanke Isra’ila
A lokacin da yake ganawa da Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, Shugaba Amurka, Joe Biden ya danganta harin makamai da aka kai a wani asibitin Gaza ranar Talata ga Falasdinawa cewa ba Isra’ila ba ce, bisa bayanan da ya samu inda Biden ya ce a cikin kalamansa – ‘dayan bangaren ne’.
Wannan lamari dai ya janyo ce-ce-ku-ce a tsakanin jama’a a yankin tare da soke taron da aka shirya yi tsakanin shugaba Biden da shugabannin kasashen Larabawa.
Shugaban ya jajanta wa Isra’ila game da harin da Hamas ta kai amma ya jaddada mahimmancin rage asarar fararen hula.
Wakilin Falasdinawa a Majalisar Dinkin Duniya, Riyad Mansoor ya nemi Amurka ta dakatar da Isra’ila kan kisan da take yi a Gaza, bayan harin asibitin da ake zargin ta kai ya hallaka fiye da fararen hula 450 zuwa ranar Laraba.