Kungiyar mabiya addinin Kiristanci ta kasa (CAN) ta nuna damuwarta kan rikicin Isara’ila da Falasdinu inda ta nuna fargabarta kan halin da masu ziyarar ibada na Nijeriya da suka tafi kasar Isra’ila ke ciki.
Shugaban kungiyar, Most Rev. Daniel Okoh, ya bayyana hakan a cikin sanarwar da ya fitar a ranar Laraba a Abuja.
- Gwamnatin Tarayya Za Ta Dauki Matasa Miliyan 5 Aiki A Sabon Shirin N-Power – Minista
- Dan Kwallon Nijeriya Na Cikin Hazikan ‘Yan Wasan Bundesliga Na Watan Satumba
Kazlika, ya shawarci kamfanonin jiragen sama da ke aikin jigilar masu ziyarar zuwa Isra’ila da su dakatar, har sai komai ya koma daidai a kasar ta Isra’ila.
Okoh ya yi kira ga Isra’ila da Falasdinu da su dakatar da rikicin su rungumi tattaunawar sulhu ta hanyar diflomasiyya don kawo karshen yakin da suke yi.
Kungiyar ta kuma yi tir da duk wani nau’i na rikici wanda zai zama barazana akan rayuwar jama’ar da ba su ji ba su gani ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp