Rundunar ‘yansanda ta jihar Kano ta kama mutum uku da take zargin masu fashi da makami ne a karamar hukumar Garko da ke Jihar.
A cikin sanawar da kakakin rundunar, SP Abdullahi Kiyawa ya fitar a ranar Laraba a Kano, ya bayyana cewa, rundunar ta samu wannan nasarar ce bayan samun rahoto daga wani mai suna Nura a ranar 6 ga watan Oktoba a kauyen Kankiya a karamar hukumar Garko.
- Rikicin Isra’ila Da Falasdinu: CAN Ta Bayyana Damuwarta Kan Halin Da Mahajjatan Nijeriya Ke Ciki A Isra’ila
- Sakamako Da Aka Samu Bayan Gina Shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya
Kiyawa ya ce, “Nura a lokacin da ya ke kan hanyarsa ta zuwa jihar Kaduna don yin kasuwanci sai ‘yan fashin suka yi masa fashin Naira miliyan 2.9 akan hanyar Garko bayan ya bar gidansa.
“Bayan da rundunar ta karbi rahoton na sa ne ta kai masa dauki aka kaishi babban asibitin Garko, inda kuma tawagar ‘yansanda bisa jagorancin DPO na Garko, ya kwashi jajamii zuwa wajen da lamarin ya auku.
“Bisa samun bayanan sirri, hakan ya sa an samu nasarar cafke wani dan shekara 25 mai suna Sunusi Yusuf wanda ya kasance aboki ne ga Nura a matsayin wanda ake zargi.
“Binciken da sashen binciken manyan laifuka na hukumar(CID) ya gudanar, ya janyo cafke wasu mutum biyu Sunusi Abubakar, dan shekara 21 da Nasiru Ibrahim dan shekara 22 a masayin sauran da ake zargi.
Kazalila, kakakin ya bayyana cewa, ‘yansandan sun kuma kwato Naira N611,000 da kwabsar albarusai guda shida na samfarin bindiga kirar AK-47 daga gun wadanda ake zargin.
Ya ce, za a gurfanar da su a gaban kotu bayan an kammala bincike.