Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya yi wani taron gaggawa don tattaunawa kan rikicin da ke faruwa tsakanin Isra’ila da Falasdinawa a Zirin Gaza.
Jakadan Majalisar mai kula da al’amuran Gabas ta Tsakiya, Tom Wenneslan, ya yi gargadin cewa, tsagaita wutar da bangarorin biyu suka yi ba mai dorewa ba ne.
Don haka, dole ne a nemo mafita a siyasance kafin bangarorin biyu su sake komawa filin daga Wanda hakan ba zai bada damar lalubo mafita a siyasance ba.
Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa, Jakadan Rasha Vasisily Nebenzia a taron, ya nuna damuwarsa na tabarbrewar rikicin, wanda ya ce hakan na iya haifar da babbar matsala ta jinkai da yanzu ake fama da ita a zirin Gaza.
Akalla Falasdinawa 44 wadanda yawancinsu fararen hula ne da kuma yara 15 ne suka rasa rayukansu a lokacin da Isra’ila ta soma ruwan bama-bamai a wuraren da kungiyar Islamic Jihad ta ke a yankin Gaza, a ranar Juma’a.