• English
  • Business News
Saturday, October 25, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Rikicin Kabilanci: An Fara Binciken Wasu Manyan Sarakuna A Kogi

by Sadiq
3 years ago
Sarakuna

Gwamnatin Jihar Kogi ta fara gudanar da bincike a kan wasu manyan sarakunan Jihar guda biyu game da wani mummunan tashin hankalin da ya yi sanadin mutuwar akalla mutane tara tare da kone gidaje da dama  a karamar hukumar Bassa da ke jihar.

Rahotanni dai sun nuna cewa manyan sarakunan guda biyu, masu daraja ta daya sun hada da Alh. Khalid Ali Bukar Sarkin Mozum, Sarkin Bassa da kuma Chif William Keke dukansu a yanzu haka suna hannun hukumomi a jihar domin gudanar da bincike a kan lamarin.

  • ‘Yan Bindiga Sun Sace DPO A Kaduna
  • G7 Ta Sha Alwashin Ci Gaba Da Taimakon Ukraine A Yakinta Da Rasha

Gwamnatin jihar dai ta ce yankin na Bassa ya dade yana fama da tashin hankali da ya shafi kabilanci da kuma rikicin mallakar filaye a tsakanin ‘yan kabilar Egbira da kuma Bassa Komo.

Al’amarin da gwamnatin jihar ke gani sarakunan na da rawar takawa wajen shawo kan wannan matsala kamar yadda kwamishinan labarai na jihar Kogin Mr. Kinsley Fanwo, ya yi karin bayani, inda ya ce ba wai an kama su bane, an gayyace su ne domin su yi karin haske a kan matsaloli da dama da za su taimaka wajen dorewar zaman lafiya a wannan karamar hukuma ta Bassa.

Fanwo, ya ce gwamnati ta yi kokarin dawo da zaman lafiya a yankin, kuma akwai wani tsari da aka samar da zai hana aukuwar abin da ya faru a baya.

LABARAI MASU NASABA

Bankin Providus

Hukumar NASENI

Daya daga cikin sarakunan yankin da aka kone gidansa sakamakon tashin hankalin, yanzu haka ya ke gudun hijira, wato Hakimin Mozum, Alh. Haruna Abubakar, ya ce duk da suna gudun hijira, a yanzu haka suna kokarin karbar Belin Babban sarkin nasu.

Masu sharhi a kan lamurran tsaro dai na ganin matakin rike manyan sarakunan yankin, watakila ya taimaka wajen gano bakin zaren da zai taimaka wajen shawo kan matsalar tashin-tashina da a aka dade ana fama da ita a yankin.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Labarai

Bankin Providus

October 25, 2025
Labarai

Hukumar NASENI

October 25, 2025
Labarai

Daɓid Adeyemi

October 25, 2025
Next Post
An Kashe Kasurgumin Dan Fashin Dajin Da Ya Addabi Mutane A Leren Jihar Kaduna

An Kashe Kasurgumin Dan Fashin Dajin Da Ya Addabi Mutane A Leren Jihar Kaduna

LABARAI MASU NASABA

Bankin Providus

October 25, 2025
Firaministan Sin Ya Isa Singapore Don Ziyarar Aiki

Firaministan Sin Ya Isa Singapore Don Ziyarar Aiki

October 25, 2025

Hukumar NASENI

October 25, 2025
An Gudanar Da Taron Cika Shekaru 80 Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan Da Dawo Da Shi Kasar Sin A Beijing

An Gudanar Da Taron Cika Shekaru 80 Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan Da Dawo Da Shi Kasar Sin A Beijing

October 25, 2025

Daɓid Adeyemi

October 25, 2025
Wakilin Sin: Shawarar GGI Ta Nuna Yadda Za A Jagoranci Bunkasa Makomar MDD

Wakilin Sin: Shawarar GGI Ta Nuna Yadda Za A Jagoranci Bunkasa Makomar MDD

October 25, 2025
Gwarzuwar Ma’aikaciyar Jinya Ta Shekarar 2025: Misis Mabel Ijeoma Duaka

Gwarzuwar Ma’aikaciyar Jinya Ta Shekarar 2025: Misis Mabel Ijeoma Duaka

October 25, 2025
Kasar Sin Ta Tsara Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar-biyar Na 15

Kasar Sin Ta Tsara Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar-biyar Na 15

October 25, 2025
Gwarzon Mai Koyar Da Wasanni Na Shekarar 2025 Justine Madugu

Gwarzon Mai Koyar Da Wasanni Na Shekarar 2025 Justine Madugu

October 25, 2025
An Kaddamar Da Nuna Muhimman Shirye-shiryen CMG A Membobin APEC

An Kaddamar Da Nuna Muhimman Shirye-shiryen CMG A Membobin APEC

October 25, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.