A rana ita yau Juma’a ne, kotun daukaka kara da ke babban birnin tarayya Abuja, ta yanke hukuncin cewa; babbar kotun tarayya, ba ta da hurumin sauraron karar da ta shafi soke masarautun jihar; wanda ko shaka babu, hakan ya tayar da rudani.
Rikicin ya shafi nadin Muhammadu Sanusi II, a matsayin Sarkin Kano na 16 tare kuma da soke Masarautun Kano biyar da dokar Masarautun Kanon ta 2019 ta nada. Hukuncin nata ya shafi hukunce-hukunce biyu guda da aka yanke a kotuna biyu da ke birnin Kano, wato babbar kotun tarayya da ke Kano da kuma babbar kotun jihar ta Kano.
- Bajintar Aiki: Majalisar Dattawa Ta Jinjina Wa Ministan Yaɗa Labarai
- ‘Yan Bindiga Sun Harbi Likita Tare Da Garkuwa Da Ma’aikatan Jinya A Wani Harin Asibiti A Katsina
A hukunci na farko, kotun ta yanke hukuncin cewa; babbar kotun gwamnatin tarayya, ba ta da hurumin tsoma baki a rikicin Masarauta. Kotun ta kara da cewa, babbar kotun Kano ce kadai take da hurumin yanke hukunci a kan duk wani rudani da ya shafi sarauta a Jihar Kano. Sai dai, an samu sabani tsakanin
Alkalai uku da suka yanke hukunci a kan lamarin.
Mai shari’a Gabriel Kolawale, wanda shi ne ya karanto hukuncin; ya umarci a mayar da karar zuwa kotun da ta dace, wato babbar kotun Kano; domin ci gaba da sauraron karar. Inda kuma sauran Alkalan biyu suka ki amincewa da batun mayar da karar zuwa babbar kotun jihar ta Kano tare da bayar da umarnin watsi da batun shari’ar baki-daya.
A hukunci na biyu kuma, kotun daukaka karar ta yi watsi da matakin babbar kotun Kano, na haramta wa Aminu Ado Bayero da sauran sarakuna hudu na jihar; bayyana kansu a matsayin sarakuna.
Kotun karkashin jagorancin mai Shari’a Mohammed Mustapha, ta bayyana cewa; akwai kuskure a hukuncin babbar kotun ta Kano na ranar 15 ga watan Yulin 2024, sannan kuma ya saba wa ka’idar jin ta kowane bangare.
Har ila yau, kotun ta kuma umarci Alkalin kotun ta Kano; ya mika shari’ar ga wani Alkalin na daban, domin sake sauraron shari’ar daga farko. Kazalika, kotun daukaka karar ta bayyana ce; hukuncin kotun ta Kano na cike da “Rashin adalci da saba ka’idar bai wa kowane bangare dama”.
Kotun ta kara da cewa, “Babbar Kotun Kano; ta ci gaba da sauraron karar ne ba tare da sanar da Aminu Ado Bayero rikicin Masarautar Kanon na baya-bayan nan ya samo asali daga matakin da gwamnatin jihar ta dauka a 2023 ba, inda gyaran da majalisar dokokin jihar ta yi wa dokar masarautun jihar; ta kuma bai wa gwamnan jihar damar rushe masarautu biyar na jihar ta Kano.
Wannan dalili ne ya bai wa Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf damar sauke Aminu Ado Bayero da sauran Sarakunan Masarautun Bichi, Gaya, Karaye da kuma Rano daga kan mukamansu.
Mun Shirya Tsaf Don Tunkarar Kotun Koli – Dan’agundi
Sarkin Dawaki Babba, Alhaji Aminu Babba Dan’agundi; wanda ya yi karar Gwamnatin Jihar Kano, kan batun rikicn masarautar, a ranar Lahadin da ta gabata; ya bayyana cewa, za su daukaka karar shari’ar Masarautar Kano zuwa Babbar Kotun Koli.
Aminu Babba, ya bayyana haka ne; a lokacin wani taron manema labarai da ya kira, domin yin karin haske kan hukuncin kotun da ake ta faman muhawara a kai a Kano, ya ce “Babu wani Alkali a duniya da zai kalli wannan shari’a ya ce, ba Alhaji Aminu Ado Bayero ne Sarkin Kano ba. Sai dai, idan kotun daga ke sai Allah ya isa ce ta ce, ba shi ne sarki ba; daga nan kuma sai mu mayar da komai ga Allah SWT”, in ji Dan’agundi.
A bangare guda kuma, fitaccen Lauya kuma mai fashin baki kan harkokin shari’a; Abba Hikima Fagge, ya yi sharhi tare da fadin albarkacin bakinsa; kan wannan dambarwa ta shari’ar Masarautar Kanon, inda ya bayyana cewa; kowane bangare ko tsagi na da dalilin yin murna ko cewa shi ne ya yi nasara a wannan hukunci da kotu ta yi.
Fagge ya kara da cewa, akwai kararraki guda biyu da aka shigar, akwai wadda aka shigar kotun gwamnatin tarayya, amma ita ba a yanke hukuncin har karshe ba, duk da cewa kuma an samu oda ko umarnin da ya hana gwamnati yin wani abu a kan wannan doka da aka yi sabuwa, akwai kuma wadda ta ce; duk wani abu da aka yi sabanin abin da ake kai a shekarar 2024, dokar ta bayyana shi a matsayin rusasshe, sai kuma batun amincewar da kotun ta yi na cewa tana da hurmin sauraron wannan kara, amma dai wannan kwarya-kwaryar hukunci ne.
Sai kuma, bangaren Sanusu Lamido Sanusi; akwai karar da suka shigar, inda gwamnatin Kano ke neman kotu ta hana Sarakunan nan hudu; ciki har da Aminu Ado Bayero, bayyana kansu a matsayin Sarakuna masu daraja ta daya tare kuma da tabbatar da nadin da aka yi wa Sunusin a matsayin Sarkin Kano.
“Don haka, idan za a iya tunawa; kotu ta yanke hukunci tare da bayyana cewa, lallai nadin da aka yi wa Sanusi yana nan a kan doka; sannan ta kuma sanar da cewa, ta dakatar da Alhaji Aminu Ado Bayero da sauran Sakuna hudu daga ayyana kansu a matsayin Sarakuna masu daraja ta daya.” Saboda haka, shi ma wannan wani abu ne da ake ganin yanzu an warware shi; domin kamar wani ta kunkumi ne da aka sanya wa Aminu Ado Bayero, in ji Fagge.
Har ila yau kuma, masu cewa kotu ta kori karar; shi ma ba zai hana Muhammadu Sanusi yin wani abu ba. Domin kuwa, karar da Jihar Kano ta shigar, wadda aka ce akwai tauye hakkin wani da aka yi; an ce a koma a sake saurarar karar. Kana kuma, an cire wa Gwamnatin Jihar Kano, wani takunkumi ita ma.
Saboda haka, idan ka kalli wadannan abubuwa guda biyu, za a iya cewa; kowa a cikinsu ya samu nasara, sannan kuma akwai wani abu guda wanda yake da muhimmanci, idan gwamnati ta yi wani abu za a kaddara cewa, wannan abun daidai ne har sai an samar da wani abu ko kotu ta ce abin ba daidai ba ne.
Don haka, ta wannan bigere Gwamnatin Kano da Majalisa sun yi doka ta rushe masarautu tare da nada Muhammadu Sunusi II, a nan a doka wannan abu za a iya cewa; daidai ne har sai an samu kotu ta ce ba daidai ba ne.
Har ila yau, hukuncin da ya ce ba daidai ba ne, yanzu shi ma an soke shi, don haka kenan wannan nadin da aka yi; zai tsaya sannan kuma dokar da majalisa ta yi tana nan. Sai dai kuma, wani abu da ya kamata a kalla shi ne; wanda kuma ba za a ce ya tsaya dari bisa dari ba, furucin kotun na cewa; a koma a sake shari’a da aka yi a kotun Jihar Kano, na cewa ka da Aminu Ado Bayero ya sake kiran kansa a matsayin Sarkin Kano, a cewar Abba Faggen.
Wannan dambarwa dai, na ci gaba da yamutsa hazo a halin yanzu, musamman a bangaren da ya shafi siyasar Kano, kowane bangare na yada wa masoyansa cewa; shi ne ya yi nasara a wannan shari’a, duk kuwa da cewa; masanin shari’ar Abba Hikima Fagge, tuni ya bayyana abin da ya fahimta da shari’ar cewa dai, “Ba a san ma ci tuwo ba, hai sai miya ta kare”.