Rikicin cikin gida na jam’iyyar NNPP a Jihar Kano, ya kara tsamari bayan ɗaya daga cikin shugabannin jam’iyyar, Sanata Jibrin Doguwa, ya yi watsi da korar ɗan majalisar tarayya Abdulmumin Jibrin Kofa.
Doguwa ya ce korar ba ta dace ba domin ba bisa dokokin jam’iyyar aka yi ba.
- Neman Gurbin Kofin Duniya: Arokodare Ya Farfaɗo Da Mafarkin Nijeriya A Wasan Rwanda
- Dorad Da Zuba Jari A Sashen Bincike Da Samarwa Da Kare Ikon Mallaka Sun Taimaka Wa Sin Zama Kan Gaba A Duniya Ta Fuskar Kirkire-kirkire
Wannan martanin nasa ya biyo bayan zargin da tsagin shugabancin jam’iyyar ɓangaren Kwankwasiyya, Hashim Dungurawa, ya yi wa Jibrin na aikata ayyukan da suka saɓa wa jam’iyya da kuma ƙin biyan kuɗin jam’iyya.
Sai dai Doguwa ya ƙaryata wannan batu, inda ya ce Jibrin bai aikata wani laifi ba.
Ya kare hirar talabijin da Jibrin ya yi wacce ta janyo cece-kuce, inda ya jaddada cewa ba ta saɓa wa muradun jam’iyyar ba.
“Abin da Jibrin ya faɗa ba wai adawa da jam’iyya ba ne. Kowane ɗan siyasa yana da ‘yancin sauya jam’iyya. Ko Shugaba Bola Tinubu ya taɓa sauya jam’iyya kafin ya zama shugaban ƙasa,” in ji Doguwa.
Ya kuma gargaɗi Dungurawa da ya daina korar ‘ya’yan jam’iyyar ba bisa ƙa’ida ba, inda ya ce za su kai ƙara kotu idan ɓangaren nasa ya ci gaba da yin haka.
Wannan sabon rikici ya sake nuna yadda NNPP ke ƙara tarwatsewa a Kano tun bayan zaɓen 2023, inda har yanzu ake taƙaddama kan shugabanci.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp