Ba tare da wata alama ta kawo karshen rikicin shugabanci da ke kara ta’azza a jam’iyyar PDP, rahotanni sun bayyana cewa bangaren jam’iyyar da Mohammed Abdulrahman ke jagoranta, wanda ke samun goyon bayan ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, na shirin gudanar da sabon babban taronta na kasa don yin martani ga taron da aka gudanar a watan da ya gabata a Ibadan, babban birnin Jihar Oyo.
Don sauya sabon tsarin samar da wani rukuni na jami’an jam’iyyar na kasa, an gudanar da taro a ranar Lahadi a gidan ministan Abuja. A cikin mahalartan taron akwai ‘yan majalisar tarayya masu ci da wasu daga cikin mambobin kwamitin zartarwa na kasa da shugabannin jihohi da sauransu.
- Da Ɗumi-ɗumi: PDP Ta Kori Wike, Fayose, Anyanwu Da Wasu Mutane 7
- Atiku Ya Fice Daga PDP Saboda Na Ƙi Bari Ya Lalata Mana Jam’iyya – Wike
An gani a taron inda aka yanke shawarar gudanar da sabbin tarukan jam’iyya a jihohin da ba a gudanar da irin wannan taron ba, sun hada da shugaban jam’iyyar PDP, Abdul Rahman Mohammed da shugaban kwamitin amintattu, Sanata Mao Ohuabunwa da sakataren jam’iyyar na kasa, Sanata Samuel Anyanwu da tsohon sanatan Abuja, Philip Tanimu Aduda da tsohon gwamnan Jihar Abiya, Okezie Ikpeazu da mai masaukin baki, Nyesom Wike.
Yayin da yake jawabi a taron, shugaban kwamiti amintattu, Sanata Ohuabunwa, ya ce shugabancinsa ya himmatu tare da kwamitin zartarwa a jam’iyyar don tabbatar da cewa duk matakan da aka dauka sun bi tsarin doka da ka’idojin jam’iyya, da kuma dokar zabe.














