ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

2027: ADC Ta Caccaki Tinubu Kan Azarbabin Fara Yakin Neman Zabe

by Leadership Hausa
9 months ago
ADC

Jam’iyyar hadaka ta ADC ta caccaki Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu bisa zarginsa da karkatar da hankalin al’umma daga matsalar tsaro da ke ta kara tabarbarewa a Nijeriya ta hanyar fara yakin neman sake zabensa a shekarar 2027 tun kafin lokaci ya yi.

Jam’iyyar ta ce matakin ba wai kawai yana lalata lamarin ba ne har ma da ingancin tsaro da shugaban kasa da kansa ya ayyana.

  • Tsohon Gwamnan Kaduna, El-Rufai, Ya Fice Daga SDP, Ya Koma ADC
  • 2027: Ganduje Ya Gargaɗi Mambobin APC Kan Fara Tallata Masu Neman Takarar Gwamna Da Wuri

A cikin wata sanarwa da sakatare yada labarai na jam’iyyar ADC, Malam Bolaji Abdullahi, ya sanya hannu, jam’iyyar adawa ta yi suka ga rahotannin da ke cewa shugaban kasa ya rarraba motocin da ke da alama ga yada siyasa karkashin shirinsa na ‘Ambassadors na Sabon Fata’ a fadin kasar nan.

ADVERTISEMENT

Ya yi gargadin cewa irin wannan aiki ya keta jadawalin kamfen din hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) kuma yana kawo damuwa ga tsarin mulki a wannan lokaci.

A cewar Abdullahi, wannan lamari na ci gaba da jefa shakku kan kokarin gwamnati wajen magance rashin tsaro da ke kara ta’azzara wanda ya sa da dama daga cikin ‘yan Nijeriya an yi garkuwa da su da tilasta musu na barin gidajensu da kuma gudanar da rayuwa cikin tsoro.

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi

“Jam’iyyar hadaka ta ADC tana cikin matukar damuwa da rahotannin da ke cewa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya raba jerin manyan motoci kirar Hilud, Land Cruiser, da motoci masu daukar fasinja kirar Hummer ga wakilan siyasa a fadin kasar nan, ta haka ne ya fara kamfaninsa na neman sake zabensa a 2027,” in ji Abdullahi.

Jam’iyya ta bayyana cewa yayin da kasar ke bukatar karfafa matakan tsaro da mayar da hankali ba tare da jinkiri ba wajen dawo da aminci, amma gwamnati na ci gaba da gudanar da ayyukan siyasa na yau da kullum duk da yadda mawuyacin halin da ‘yan kasa suke ciki.

“Yayin da a kullum ‘yan kasa na fama da matsalar garkuwa da mutane da kashe-kashe da yin kaura a daidai wannan lokaci kuma shugaban kasa ya raba motocin siyasa,” in ji Abdullahi.

ADC ta jaddada cewa kasar na bukatar a dauki matakan gaggawa kan shugabanci, ba kawai gudanar da sha’anin siyasa ba.

Jam’iyyar ta kuma bayyana Tinubu ya zama shugaban Nijeriya na farko da aka zaba da ya ayyana dokar ta-baci kan tsaro, yayin da ake zarginsa fara yakin nema zabe tun kafin lokaci ya yi.

Ya yi kira ga INEC da ta dauki matakan gaggawa don magance abin da ta bayyana a matsayin kararar doka a tsarin zabe.

ADC
Leadership Hausa
Website |  + postsBio
  • Leadership Hausa
    Karuwar Farin Jinin Gwamna Umaru Bago A Siyasar Jihar Neja
  • Leadership Hausa
    Kyakkyawan Tsarin Laken Asiri Zai Dakile Shirin Magudin Zabe A Nijeriya —Mohammed
  • Leadership Hausa
    Batun Dawo Da Tallafin Mai Da Atiku Ya Yi Na Ci Gaba Da Tayar Da Kura
  • Leadership Hausa
    Batun Guguwar Kakar Yakin Neman Zabukan 2027 A Nijeriya

MASU ALAKA

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027
Siyasa

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi
Manyan Labarai

2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi

September 8, 2026
ADC
Siyasa

Muna Da Yan Takarar Gwamna A Jihohi 28 Don Shiga Zaben 2027

September 6, 2026
Next Post
Dawo Da Martabar Birnin Abuja Ta Hanyar Doka Da Oda Shi Ne Babbar Burin Wike – Mukthar Galadima

Dawo Da Martabar Birnin Abuja Ta Hanyar Doka Da Oda Shi Ne Babbar Burin Wike - Mukthar Galadima

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.