Ana ci gaba da wani taron gaggawa na gwamnonin jam’iyyar APC mai mulki a sakatariyar jam’iyyar ta kasa da ke Abuja.
Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, ne ya kira taron domin tattauna batutuwan da suka shafi yakin neman zabe, rikicin Naira da kuma zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya da za a yi a ranar Asabar mai zuwa.
- Ku Zabi Tunibu Na Yi Imani Zai Dora Daga Inda Na Tsaya — Buhari
- Gwamnatin Tarayya Ta Mayar Wa Da El-rufai Martani Kan Zargin Yi Wa Tunibu Zagon Kasa
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an tsaurara matakan tsaro a ciki da wajen sakatariyar yayin da ake ci gaba da gudanar da taron na sirri.
Gwamna Nasir El-Rufai (Kaduna), Abdullahi Sule (Nasarawa), Bello Matawalle (Zamfara) da Simon Lalong (Plateau) da kuma Mai Mala Buni (Yobe) na daga cikin gwamnonin da suka halarci taron.
A jawabinsa na bude taron, Adamu ya ce, “Na yi farin ciki da amsar da aka bayar kawo yanzu. Kuma ni a fahimtata da yawa daga cikin gwamnonin suna kan hanyarsu ta zuwa. Nasan kuna sane da dalilan da suka wajabta buƙatar wannan gayyata sakamakon yadda lamura suke tafiya a yanzu.
“Ba ma son zama a yanke hukunci ga kowa ko hukumomi game da abin da ke faruwa a kasar a yau kamar yadda lamarin ya shafi babbar jam’iyyarmu.
“Na ga abin da ya fi dacewa a yi shi ne a samu duk masu rike da madafun iko a cikin jam’iyya, mu hadu a yi mu’amala da juna ta yadda za mu iya samun kyakkyawar matsaya don magance yanayin da muke ciki.”
Wasu gwamnonin jam’iyyar APC sun shigar da kara a gaban gwamnatin tarayya kan batun sake fasalin naira.
Kotun koli ta umarci CBN da kada ya aiwatar da wa’adin amma Godwin Emefiele, gwamnan CBN ya ce babu bukatar a canza wa’adin.
Buhari dai ya bi umarnin kotu ta wani bangare bayan da ya bayar da umarnin tsawaita wa’adin Naira 200 tare da bayyana cewa tsofaffin takardun N500 da N1000 a dakatar da karbarsu.
Hakan ya jawo cece-kuce a fadin kasar. Gwamnonin jam’iyya mai mulki sun bi sahun masu sukar Buhari kan lamarin.
Yayin da Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi zargin cewa manufar sake fasalin Naira na da nufin durkusar da dimokuradiyyar Nijeriya, takwaransa na Kaduna, Nasir El-Rufai, ya bukaci mazauna yankin da su yi watsi da umarnin Buhari.
Gwamna Dapo Abidoun (Ogun) da Babajide Sanwo-Olu (Lagos), Abubakar Badaru (Jigawa) na daga cikin wadanda suka bayyana cewa har yanzu ana amfani da tsofaffin takardun kudi na N500 da N1000 a jihohinsu.