‘Yan majalisaar dokokin Jihar Nasarawa sun cimma yarjejeniya kan jagorancin majalisan karo na bakwai, wanda tun a watan shida na shekarar 2023 ake ta fama da rikece-rikice dangane da wanda zai jagoranci majalisaar.
Rikici ya-ki-ci-ya-ki-cinyewa tsakanin Hon. Balarabe Abdullahi na jam’iyyar APC mai wakiltan mazaber Omasha da takwararsa Hon. Daniyel Oga Ogazi na jam’iyyar APC mai wakiltan mazaber Kokona ta gabas.
A ranar Juma’a da ta gabata, Hon. Daniyel Oga Ogazi ya shaida wa manema labarai cewa ya janye daga wannan rikici, domin samar da maslaha na ci gaban Jihar Nasarawa.
Ogazi ya ce shi mai biyayya ne kuma masu ruwa da tsaki a kasa sun tsoma baki, sannan sarakuna da shugabannin siyasa na Jihar Nasarawa sun shiga tsakani.
Dukkan bangarorin biyu sun janye karar da suka shigar a gaban kotu, sun amince da sake gudanar da zabe mai inganci domin ci gaban Jihar Nasarawa.
Hon. Daniyel Ogazi ya bayyana janyewarsa daga sake tsayawa takarar, kuma zai iya mara wa duk wanda ya yi nasara baya domin ci gaban al’ummar Jihar Nasarawa.
Bayan rantsar da ‘yan majalisar, an kuma gudanar da zabe a zauren majalisar dokokin da mutum 24, inda suka sake zaben Hon. Balarabe Abdullahi na jam’iyyar APC mai wakiltar Umasha a matsayin kakakin majalisan dokokin Jihar Nasarawa. Yayin da aka zabi Abel Bala na jam’iyyar PDP a matsayin mataimakin kakakin majalisan karo na bakwai.