Wannan adadi na zuwa ne jim kadan bayan da Gwamna Aminu Masari na jihar ya aike da tawaga karkashin jagorancin sakataren gwamnatin jihar Alhaji Muntari Lawal domin jajantawa iyalan wadanda lamarin ya shafa.
Mazauna yankunan da lamarin ya shafa sun ce adadin wadanda suka mutu ya haura dari, inda suka ce, ana ci gaba da zakulo wasu gawarwaki daga yankin da abin ya faru, sabida har yanzun ba’aga wasu mutanen yankunan ba.
Daya daga cikin mazauna kauyen Guga, Abubakar Hashimu, ya shaida wa gidan talabijin na Channels cewa ko a ranar Juma’a an yi jana’izar mutane 63, kuma a ranar Asabar ma an ciko wata mota dauke da gawarwaki sama da 30, har yanzu muna sa ran ganin wasu karin gawarwakin”.
A cewar Hashimu, sama da 100 ne suka mutu ya zuwa yanzu.
A cewar majiyoyi, lamarin ya faru ne a ranar Alhamis bayan da ‘yan ta’addan suka yi awon gaba da shanu da dama na mutanen yankin a ranar Laraba.