Hukumar Hisba, hukuma ce da ke da hurumi a Shari’ar Musulunci, kasancewar babban aikinta shi ne umarni da aikin alhairi da kuma hani da mummunan aiki, an kaddamar Hukumar Hisba tun lokacin zangon farko na Gwamna Kwankwaso, amma ta samu cikakken gindin zama a shekara ta 2007 zamanin Mulkin Malam Ibrahim Shekaru inda Shugaban Hukumar Hisba na farko shi ne Sheikh Malam Yahaya Farouk Chedi bayan shi Kuma Malam Ibrahimahim Mai bushira.
Hukumar Hisba a Jihar Kano ba yanzu shugabaninta suka fara gamuwa da tunzuri daga wasu mutane da ke ganin aikin na Hisba na yin katsalandan ga sana’unsu ko ra’ayinsu, Malam Abdulkarin Abubakar Rabo wanda har wata wakar cin zarafi taron wasu mawaka suka yi masa saboda kawai ya matsa lamba kan daidaita sahun wasu rukunin al’umma da ake ganin suna kokarin gurbata tarbiyyar yara musamman mata.
- Kano Za Ta Haɗa Gwiwa Da Afrinvest Don Haɓɓaka Kasuwanci Da Ci Gaban Jihar
- Yadda Sheikh Daurawa Ya Koma Ofis Bayan Sulhu Da Gwamnan Kano
Bayan samun sauyin Gwamnati ne kuma Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya sake darewa an karagar mulkin Kano kuma ya nada sabon Shugaban Hukumar ta Hisba Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, wanda kowa ya san shi mai goyon bayan Darikar Kwankwasiyya ne, sannan kowa ya san Daurawa a matsayin wanda ya samar da gagarumin ci gaba a harkokin gudanarwa hukumar, ciki har da nasarar bijiro da shirin auren zawarawa wanda ya dauki hankalin duniya baki daya.
Halin da ake abin ya zama sahun gaba cikin abubuwan da dake daukar hankali a Kano bai wuce batun murabus din Daurawa ba, sakamakon jawabin da Gwamnan ya gabatar a lokacin taron daukacin mala-man addini da limamai da ya gudana a fadar Gwamnatin Kano, inda Gwamnan ya bayyana matakn Hukumar Hisba na yaki da badala da cewa bai ji dadin abin da ya gani a wani faifan bidiyo dake nuna ana dukkan matasa da gorori tare da rungumar mata ana jefa su cikin motar Jami’an Hisba.
Jin wannan kalamai na Gwamna na Kano ne ya sa Sheikh Daurawa bayyyana murabus daga mukaminsa na babban Kwamandan Hisba, inda ya bai wa gwamna hakuri tare da rokon afuwarsa, sannan ya.
Lamarin da ake alakanta shi da fitsararriyar ‘yar TikTok Murja Kunya wadda ta shahara ta fuskar fitsara batsa da Kuma yadda wasu mazauna Unguwar Hotoro Suka yi kararta sakamakon yunkurin bata tarbiy-yar yaransu, hakan ta sa aka shelanta farautarta, wanda kuma jami’an na Hisba suka samu nasarar damke ta tare da gurfanar da ita gaban kuliya, inda daga nan alkalin kotun ya aika da ita gidan gyaran hali har zuwa lokacin da za’a dawo da ita kotu.
Amma wani abu mai kama da al’amara kawai sai aka wayi gari da jin labarin fitar da ita ba kuma tare da sanin alkalin da ya aikata Gidan Gyaran Halin ba.
Bayyana murabus din Daurawa ne ya sanya Limaman masallatan Juma’a Suka gabatar mafi yawan Hud-ubarsu kan wannan matsàla. Sai dai wasu Malamai na ta rokon Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa da dubi girman Allah ya koma bakin aikinsa. A washe garin murabus din na Daurawa wata majiyar ta Shaida wa Jaridar LEADERSHIP Hausa cewa an kwashe awa bakwai na gudanar taro kan lamarin
Babu shakka kalaman na Gwamnan Abba Kabir Yusuf ya zama abin da ko ina a Kano ke zaman abin tattaunawa, wasu na ganin barin tantiriyar ci gaba da wannan mummunar ta’adar zai kara zubarwa da Jihar Kano kimar da aka Santa dashi
Sheikh Daurawa Ya Amince Da Komawa Kan Mukaminsa
Sakamakon wani zama na musamman da wasu Malamai suka yi da Gwamnan Jihar Kano, an samu sasanci, yanzu Shaikh Aminu Daurawa zai ci gaba da shugabancin Hukumar Hisba a Kano,
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ranar Litinin, ya bayyana cewa akwai wani zama da ya gudana tsakanin Gwamna Abba Kabir Yusuf da wata tawagar Malamai, wadanda suka hada da shi kan sa Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa bisa jago-rancin Dakta Musa Borodo da sauran Malamai irin su, Dakta Sa’idu Ahmad Dukawa, Sheikh Abdul-wahab Abdallah, Farfesa Salisu da sai sauransu.
A ta bangaren Gwamnati kuma, bisa jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf, akwai mataimakinsa, Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo, Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano, Alhaji Jibrin Ismail Fal-gore; Sakataren Gwamnatin Jihar Kano Dakta Baffa Abdullahi Bichi, da Shugaban Ma’aikatan gidan Gwamnatin jihar, Alhaji Shehu Wada Sagagi.
Yanzu dai abin da yage shi ne sauraron jin irin salon da Kwamanda Hisbar Aminu Daurawa zai shigo da shi, shin ya gindaya wani sharadi ne kan daina yi wa ayyukan hukumar katsalandan da kokarin daurewa masu badala gindi, ko kuma an yi masa iyaka kan ayyukan na Hisba, wannan dai ta Bahaushe “Maji ma-gani, an binne tsohuwa da rai.