Firaministan kasar Slovakia Robert Fico ya tattauna tare da wakiliyar kafar CMG a kwanan baya, inda ya yi nuni da cewa, idan kasashen yammaci sun ci gaba da tallafa wa Ukraine kamar yadda suke yi yanzu, to, da wuya a dasa aya ga rikicin. Ya yi fatan a daina samar da gudummawar soja ga Ukraine, don a koma teburin shawarwarin shimfida zaman lafiya, duk da cewa hakan ba abu ne mai sauki ba. A cewarsa, yin fito na fito a tsakanin sojojin Rasha da Ukraine ba shi da ma’ana.
Mr. Robert Fico ya ce, a matsayinta na makwabciyar Ukraine, kasar Slovakia tana goyon bayan kasar Ukraine. Sai dai a kan batun kungiyar NATO, yana kallon shigar Ukraine cikin kungiyar zai kasance mafarin yakin duniya na uku.
Ya ci gaba da cewa, matukar yana kan kujerar firaministan kasar Slovakia, lallai zai fito da muryar kasarsa, wato Ukraine ba za ta iya zama a karkashin inuwar NATO ba, saboda hakan na iya kara ta’azzara yanayin da ake ciki. Ya kuma ce, Ukraine na iya zama mambar kungiyar tarayyar Turai, amma tabbas ba za ta zama mamba ta NATO ba. (Lubabatu Lei)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp