Wata roka mallakar wani kamfani mai zaman kansa na kasar Sin da aka kera domin kasuwanci, ta yi nasarar harba taurarin dan adam 6 zuwa sararin samaniya a yau Asabar.
Rokar mai lakabin ZQ-2E Y2, ta harba taurarin ne da misalin karfe 12:12 na rana, daga yankin gwaji na kirkire-kirkiren kumbunan kasuwanci na Dongfeng dake kusa da cibiyar harba taurari ta Jiuquan. Rokar wani samfuri ne na ZQ-2 da aka yi wa gyare-gyare, wanda kamfanin kera rokoki mai zaman kansa dake da hedkwata a birnin ya samar.
A cewar kamfanin, rokar na iya harba kumbo mai nauyin ton 4 zuwa nisan kilomita 500 a da’irar rana.
Kafin aikin na yau, kamfanin ya yi nasarar kaddamar da rokar ZQ-2 Y1 da aka yi wa gyare-gyare a watan Nuwamban 2024, inda ya harba taurarin dan adam biyu zuwa da’irarsu.
Kamfanin ya ce an daukaka sabuwar rokar akan samfurinta na baya, kuma cikin abun da aka yi har da inganta injin tada rokar da hada wasu kayayyakin da za su maye gurbin karafa wajen jure iska domin taimakawa inganci da karfin aikinta. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp