Dan wasan gaba na Manchester United, Cristiano Ronaldo, ya sha gaban abokin hamayyarsa, Lionel Messi da Neymar da Kylian Mbappe a matakin mafi tarin jama’a tsakanin ‘yan kwallon kafa a shafin sada zumunta na Instagram.
Ronaldo ya samu karin mabiya sakamakon gasar kofin duniya da za a yi a cikin watan Nuwamba da Katar za ta karbi bakunci a 2022, kuma kyaftin din na tawagar Portugal ya samu karin mutane da ke bibiyarsa kaso 48 cikin 100 tun daga shekarar da ta gabata.
Wani bincike da Nielsen Gracenote ya gudanar ya ce dan wasan na Manchester United kan samu matsakaicin kudi da ya kai Dala miliyan 3.5 a duk sakon da ya rubuta wanda hakan ba kananan kudade bane.
Takwaran Ronaldo, dan kwallon Manchester United, Jadon Sancho shi ne kan gaba a Ingila, yayin da Gabi ya samu karin mabiya kaso 5,165 cikin 100.
Nielsen ya auna wannan ci gaban kan ma’aunin da ya tantance yawan magoya baya da karin mabiya da dan wasa ke samu da yadda ake bibiyar sa da kudin da dan kwallo ke samu a duk lokacin da ya wallafa abu a Instagram.
An kuma dora ma’aunin kan ‘yan wasan da za su wakilci kasashensu a gasar kofin duniya da za a yi cikin watan Nuwamba.
Ronaldo yana da mabiya miliyan 480 a Instagram, kyaftin din Argentina, Messi ne ke biye da shi mai mabiya miliyan 360, wanda ya samu karin kaso 38 cikin 100 – mai karbar Dala miliyan 2.6 a duk sakon da ya wallafa a kafar sada zumunta ta Instagram.
‘Yan wasan Paris St German da suka hada da Messi da Neymar da Kylian Mbappe ne ke biye da Ronaldo a mataki na biyu da na uku da kuma na hudu sai kuma sauran ‘yan wasa biyu daga PSG kan karbi matsakaicin kudin da ya kai Dalma miliyan 1 a duk sakon da suka wallafa a Instagram.
Cikin jerin 10 farko mafiya mabiya a Instagram tsakanin masu buga wasa, dan wasan Brazil mai wasa a Real Madrid, Binicius Junior ne kan gaba domin ya samu karin tarin mabiya tun daga lokacin da Real ta doke Liberpool ta lashe Champions League na 14 jumulla a kakar da ta wuce.