Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Cristiano Ronaldo, ya bayyana cewa yana son yabar kungiyar idan har an samu kungiyar da ta kawo tayin kudi.
Ronaldo, wanda ya koma United din daga Juventus a shekarar da ta wuce akan kudi fam miliyan 25 ya zura kwallaye 18 a gasar firimiyar data gabata.
Ronaldo dai yana son ya ci gaba da buga wasannin cin kofin zakarun turai na Champions league a kakar wasa mai zuwa wanda Manchester United kuma ba zata buga gasar ba bayan ta karkare a mataki na shida a kakar wasan data wuce.
A Kwanakin baya dai kungiyar ta bayyana cewa Ronaldo bana sayarwa bane sai dai wakilin sa, George Mendez ya fara tattauna wa da wasu kungiyoyin da suka hada da Bayern Munich da Chelsea da kuma AS Roma.
Kawo yanzu dai Manchester United bata sayi sabon dan wasa ba, sai dai tana tattauna wa da Barcelona domin daukar Frankie De Jong, sannan ta kusa daukar dan wasa Tyrrell Malacia daga Feyernood ya yinda kungiyar dai take neman sayan dan wasan baya na Ajax, Lisandro Martinez, dan Argentina.