Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta tabbatar da cewa a ranar Talata an yi wa dan wasanta na baya Toni Rudiger tiyata, sakamakon raunin da ya ji a gwiwa bayan dakta Manuel Leyes ya yi masa aikin a karkashin kulawar likitan Real Madrid, an kuma sanar cewar an yi aikin cikin nasara sai dai kungiyar ba ta fayyace kwanakin da zai yi jinya ba, balle a san ranar da zai koma fili.
Rudiger ya ce ya dade yana dauke da raunin, kuma haka yake buga wasa cikin radadi. ”Ina son na warke da wuri, domin akwai manyan wasannin da ke gaba na da ya hada da Nations League da kuma Club World Cup amma yanzu ina bukatar yin jinya, zan kuma yi dukkan abin da ya kamata, domin na koma fagen fama da wuri.”
- Mataimakin Shugaban Ƙasa Zai Wakilci Nijeriya A Rantsar Da Shugaban Gabon
- Shugaban NPA Dantsoho Ya Bayyana Aniyar Inganta Ayyukan Hukumar A Wannan Shekarar
An bai wa Rudiger jan kati a wasa da Barcelona, sakamakon jifan alkalin wasa, saboda ransa ya baci bisa ketar da aka yi wa Kylian Mbappe.
Barcelona ce ta yi nasara a wasan na El Clasico da cin 3-2, sannan ta lashe Copa Del Rey na 32 jimilla ranar Asabar. Daga baya Rudiger ya nemi afuwa, sai dai hukuncin laifin da dan wasan tawagar Jamus ya aikata, za a iya dakatar da shi daga buga wasa hudu zuwa 12, amma sakamakon hakurin da ya bayar aka rage hukuncin zuwa wasanni hudu. Real Madrid, wadda take ta biyu a teburin La Liga da tazarar maki hudu tsakani da Barcelona mai jan ragama, za ta karbi bakuncin Celta Bigo ranar Lahadi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp