Ruftawar masallacin kofar fadar mai martaba sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Huhu Bamalli rahoton na ci-gaba da cewa, masallata da daman gaske wadanda suka tsaya domin Sallar la’asar a babban masallacin ne suka mutu a nan take.
Adadinsu ya kai mutum hudu kuma har ya zuwa hada wannan rahoton ana ta dai tono wadanda ginin ya rufta da su.
- El-Rufai Ya Hakura Da Tayin Minista, Ya Zabi Sani Don ya Maye Gurbinsa
- Mun Dauki Darasi A Zaben 2023 – Shugaban INEC
LEADERSHIP Hausa ta samu tabbacin faruwan lamarin a yanzu haka, a yayin da wakilinta ya tuntubi ganau da ke gudanar da sana’a a kusa da masallacin a matsayin shaidun gani da ido kuma sun tabbatarwa wakilin namu cewa, akasarin wadanda ake tono ba su da rai a zahirin gaskiya, wasu kuma sun jikkata, yayin da ake kai wadanda ba su mutu ba asibiti mafi kusa domin ceto rayuwarsu.
Lamarin ya faru ne a babban masallacin juma’a da ke birnin Zazzau cikin Zariya a jihar Kaduna kuma a kusabda fadar mai martaba sarkin Zazzau.
Bayan an dauki matakin ganin an kai wanda suka rasa rayukansu ga makusantansu wasu kuma an kai su asibiti sai sarkin ya yi kira da a kauracewa yin salla a masallacin har sai a kammala gyaran masallacin.
Mai martaba ya tabbatar da rasuwar mutane hudu take wasu kuma suna asibiti don ceton rayukansu.
Bisa haka ne sarkin ya yi addu’ar samun gafara ga waranda suka rasa rayukansu kuma ya yi fatan samun lafiya ga wadanda suka samu raunuka.
Tuni sarkin ya tura injiniyoyi don su duba dukkan masallacin don daukar mataki.
Lamarin ya faru ne yayin da sarkin ya je bikin bude Masallacin a wata unguwa da ke zariya.