Bayan shafe watanni hudu ana tafka shari’a, kwamitin alkalai na mutum biyar na kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa da ke Abuja, ya saurari karar da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar da takwaransa na jam’iyyar LP, Mista Peter Obi, suka shigar a ranar Talatar da ta gabata inda zai cimma matsaya wajen zartar da hukunci.
Alkalin kotun, Mai Shari’a Haruna Tsammani ya shaida wa masu karar cewa za a sanar da su ranar da za a yanke hukunci. Kotun dai na da wa’adin zartar da hukunci har zuwa ranar 16 ga watan Satumba, bisa ga tanadin kundin tsarin mulkin kasar nan, wanda ya tanadi cewa, dole ne a saurari koke-koken zabe da kuma yanke hukunci cikin kwanaki 180 daga ranar da aka shigar da kara.
- Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka Na Kara Haifar Da Da Mai Ido
- An Kammala Harhada Tushen Sashe Na SMR A Sin
A daidai lokacin da Obi ya shigar da karar a ranar 20 ga Maris, Atiku ya shigar da kararsa ne a ranar 21 ga Maris, kusan makonni uku bayan an ayyana Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa na ranar 25 ga Fabrairu.
Idan ba a manta bai a ranar 1 ga watan Maris ne hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta bayyana dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu da kuri’u 8,794,726, yayin da Atiku da Obi suka samu kuri’u 6,984,520 da 6,101,533.
Sai dai kuma Atiku da Obi sun yi watsi da sakamakon zabe. Daga baya sun garzaya kotun sauraron kararrakin zabe domin kalubalantar nasarar Tinubu.
Masu shigar da kara guda biyu sun bukaci kotun ta soke nasarar da Shugaba Tinubu ya samu a kan dalilin da ya sa INEC ta gaza yin dukkan abubuwan da kundin tsarin mulki da dokar zabe ta tanada wajen gudanar da zaben. Sun dai bukaci ko dai kotu ta bai wa daya daga cikinsu ko kuma ta bayar da umurni a sake gudanar da zaben.
Lauyan Atiku, Chris Uche (SAN) ya sanar da kotun cewa babu dalilin da zai sa INEC ta ki yin amfani da na’ura wajen bayyana sakamakon zabe, wanda yana cikin wani bangare na sabon tsarin gudanar da zabe a kasar nan don inganta harkokin zaben Nijeriya. Ya ce rashin bin ka’ida ya turnuke harkokin zaben.
“An saka lamarin cikin sabon dokar zabe, INEC ta tabbatar mana da cewa za a yi amfani da na’urorin a zaben, wanda ka kashe naira biliyan 355 wajen sayo su, don haka ya rage wa INEC ta yi wa ‘yan Nijeriya bayani, ba wai wata matsala ce aka samu ba kawai da gangan aka yi domin yin magudin zabe,” in ji shi.
Shi ma lauyan jam’iyyar LP, Liby Uzoukwu (SAN) ya gabatar da cewa zaben da aka gudanar a rumfunan zabe 18,088, sakamakon zaben ya gurbata, zabe ne mai cike da kura-kurai. Daga cikin takardun sakamakon da INEC ta bai wa masu shigar da kara, 8,123 sun bace, wasu kuma hotuna sun tabbatar da su, ta yaya za su ce sun gudanar da sahihin zabe?
“Duk wani kwafin gaskiya na kowace takarda dole ne ya zama ainihin kwafi, wanda ke bayyana dalilin da ya sa INEC ba za ta iya fitar da asalin takardar sakamakon zabe ba saboda ba zai zama takarda mara amfani,” in ji shi.
Atiku da Obi sun yi zargin cewa rashin tura sakamakon zaben shugaban kasa ga na’ura kai tsaye daga rumfunan zabe ya haifar da rashin bin dokar zabe da ka’idojin INEC tare da samar da hanyar yin magudi.
Sai dai a nasa jawabin, lauyan hukumar INEC, Abubakar Mahmoud (SAN) ya bayya cewa, wadanda suka shigar da kara sun yi tunani a ransu cewa akwai tanadin da aka yi na watsa sakamakon zabe ta na’ura, wanda ba samu damar hakan ba. Ya kara da cewa hujjojinsu sun gaza tabbatar da yadda rashin bin ka’ida ya shafi sakamakon zaben.
Lauyan INEC ya musanta cewa kura-kuran da aka samu a lokacin zabe ba sabon abu ba ne ga na’urorin kuma ba an samu matsalar ba ne sakamakon kutse daga wasu mutane ba ne. Ya ce sakamakon da jam’iyyar LP ta fitar ba na gaskiya ba ne, domin bi yi daidai da ha hukumar zabe ba.
Ya ce amincewa da hujjar da ake bukata na samun kashi 25 cikin 100 a Babban Birnin Tarayya Abuja shirme ne kawai.
Shi kuwa lauyan jam’iyyar APC, Lateef Fagbemi (SAN) ya ce LP ta gaza tabbatar da hujjar rashin tura sakamakon zabe ta na’ura tun daga rumfar zabe. Ya ce ko an sake zaben zai kasance ne tsakanin APC da PDP.