Tun daga farkon makon nan ne aka shiga ruguntsumin rantsar da sabon zabbaben shugaban Nijeriya Asiwaju Bola Tinubu, a matsayin shugaban tarayyar Nijeriya na 16 a ranar 29 ga watan Mayu 2023.
Hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta sanar da Asiwaju Bola Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa da aka yi na shekarar 2023 in da ya lashe zaben da kuri’a 8,794,726 a takarar da ya yi a karkashin jam’iyyar APC. Bola Tinubu dai yana da shekara 70 a duniya a halin yanzu.
Ga wasu abubuwa 10 muhimmai da ya kamata al’umma su sani game da Shirin rantsar da zabbaben shugaban kasar da aka shirya yi a filin ‘Eagle Skuare’ da ke Abuja.
- Â Ana sa ran bikin zai samu halartar shugabannin kasashe 54 daga kasashen Afrika da kuma shugabanin wasu kasashen su 65 da kasashen yankin nahiyar Turai, Amurka za su halarci bikin rantsar da sabon shugaban kasar.
- Za a gudanar da taron ne a filin taro na ’Eagle Skuare’ da ke Abuja.
- Wakilan kasashe abokan Nijeriya kamar Amurka, Birtaniya, Kanada, Faransa, Saudi Arebiya, UAE, Pakistan, Chana, Jamus, Finland, Jamaica, Japan, Israila da Turkiya za su halarci taron.
- An shirya karramawa ga zababben shugaban kasa Bola Tinubu wanda kuma shi zai zama shugaban rundunar sojojin Nijeriya da fareti na musamman na ranar Talata 23 ga watan Mayu.
- A ranar 24 ga watan Mayu aka gudanar da taron majalisar zartarwa na bankwana ga ministoci a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
- Za a gudanar da taro na musamman na motsa jiki wanda bangaren matasa na jam’iyyar APC suka shirya ranar 25 ga watan Mayu a filin wasa na MKO Abiola da ke Abuja za kuma a yi addu’a ta musamman a masallacin kasa a ranar Juma’a 26 ga watan Mayu.
- Tsohon shugaban kasar Kenya, Uhuru Kenyatta, zai gabatar da lacca a kan yadda za a yi amfani da dimokradiyya wajen bunkasa ci gaba al’ummar Afrika a ranar 27 ga watan Mayu.
- Faretin yara na ranar yara ta duniya zai gudana a ranar 27 ga watan Mayu, za kuma a yi addu’o’i na musamman a babbar cocin kasa ranar 28 ga watan Mayu.
- Bikin cin abinci da nuna al’adun gargajiya a babban dakin taro na fadar shugaban kasa ranar 28 ga watan Mayu.
- Za a yi taron cin abinci na musamman da shugabannin kasa da abokan zabbaben shugaban kasa kawai za su halarta a dakin taro na fadar shugaban kasa a ranar 29 ga watan Mayu 2023.