Gamayyar wasu ƙungiyoyi biyu na jam’iyyar APC a Kano – “APC Kadangaren Bakin Tulu” da “APC ‘Yan Takwas” – sun miƙa takardar buƙatar a hukumance ga Muƙaddashin Shugaban Jam’iyyar na Ƙasa, Alhaji Ali Bukar Dalori, inda suka nemi a rushe shugabancin APC na jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abdullahi Abbas.
A cikin takardar, gamayyar ta zargi Abdullahi Abbas da mulkin kama-karya wajen tafiyar da harkokin jam’iyyar a Kano, tare da roƙon shugabancin jam’iyyar na ƙasa da ya ɗauki matakin gaggawa domin ceto jam’iyyar daga rushewa. Nura Na’annabi ne ya miƙa buƙatar a madadin ƙungiyoyin yayin wata ziyarar da suka kai shalƙwatar APC da ke Abuja.
- An Dakatar Da Shugaban APC Na Jihar Nasarawa
- Haɗakar Jam’iyyun Adawa Ba Ya Ɗaga Mana Hankali – Sabon Shugaban APC
Na’annabi ya bayyana cewa, matsalolin da suka biyo bayan rashin tsari da rashin kiyaye kalamai daga bakin Abdullahi Abbas ne suka janyo wa jam’iyyar APC rashin nasara a zaɓen 2023 a Kano. Ya ƙara da cewa idan ba a ɗauki mataki ba yanzu, jam’iyyar na fuskantar barazanar faɗuwa a 2027.
A baya-bayan nan ne gamayyar ta bai wa shugaban jam’iyyar a Kano wa’adin ya sauka daga muƙaminsa cikin mutunci ko kuma ya fuskanci shari’a, lamarin da ya nuna cewar akwai rikici mai tsanani a cikin gida a jam’iyyar a matakin jiha.
Shin ko Abdullahi Abbas zai amince ya sauka kamar yadda mai gidansa Dr. Abdullahi Umar Ganduje yayi?
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp