Bayan shafe mako guda a hannun masu garkuwa da mutane, gwamnatin jihar Edo ta ce, jami’an tsaro na musamman da suka hada da sojoji, ‘yan sanda, DSS, ‘yan banga, mafarauta da sauran jami’an tsaro sun ceto mutane 12 da aka sace a tashar jirgin kasa ta Igueben a jihar a ranar Asabar din da ta gabata.
Da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan ziyarar da yakai ma wadanda aka ceto daga hannun masu garkuwan a asibitin ‘yan sanda da ke garin Benin, babban birnin jihar a ranar Lahadi, Gwamna Godwin Obaseki ya kuma kalubalanci mahukuntan Hukumar Kula da Jiragen Kasan ta Nijeriya (NRC) kan rashin samar da isasshen tsaro a cibiyoyinta bayan harin harin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna a ranar 28 ga Maris, 2022.
Gwamnan ya kuma yi barazanar sanya wa sarakunan gargajiya takunkumi a yankin Igueben, wadanda har yanzu suke baiwa makiyaya filayen kiwo.
Gwamnan ya ce babu wani kudin fansa da aka biya domin sako wadanda aka sace, jami’an tsaro na musamman ne suka shiga dajin suka yi galaba a kan masu garkuwa da mutanen, inda suka tsare da sauran mutum biyun da suka sace, wadanda ake tsammanin cewa ma’aikatan Hukumar NRCn ne.