Bataliyar rundunar soji ta 81 ta kaddamar da bincike dangane da zargin kisan wani direba da aka gano sunansa da Lawal da ake zargin wasu sojoji da aikatawa a jihar Legas.
Lamarin ya faru ne a ranar Juma’a yayin da sojojin suka tsayar da shi Lawal a lokacin da ke kan hanyarsa ta kai wato sabuwar mota kirar Toyota Corolla ga mamallakinta a Abuja.
An yi zargin cewan sojojin sun fada ma Lawal za su daukeshi zuwa barikinsu amma sai suka wuce da shi zuwa Iyana Ipaja da ke kan hanyar Legas inda suka harbeshi tare da yasar da gangan jikinsa a daji.
Ba tare da sanin su ba, abokin Lawal wanda shi kuma yake cikin wata mota kirar Hilux ya biyo bayansa kuma ya ga dukkanin abubuwan da suka faru tare da gaggawan zuwa ya shaida wa ‘yansanda.
Abokin mamacin da ya kai rahoton faruwar labarin ga ‘yansandan, hakan ya bada dama aka bi sawun wadanda ake zargin a 9 Bridage, Maryland kuma an kai ga gano su ne a ranar Asabar.
Da ya ke maida jawabi kan wannan lamarin a yammacin ranar Lahadi, kakakin rundunar soji ta 81, Lt.-Col. Olabisi Ayeni, ya ce rundunar soji ta kaddamar da bincike kan lamarin kisan da wasu mutane sanye da kakin soja suka yi a ranar 17 ga watan Agusta.
Ayeni ya ce, “Tabbas mun kaddamar da bincike kuma za mu tabbatar da an yi gaskiya wajen zakulo makasan walau ko sojoji ne na gaskiya ko kuma wasu ne kawai suka yi amfani da kayan soji wajen aikata kisan.
“Rundunar tunin ta fara gudanar da bincike tare da hadin guiwar hukumar ‘yansanda ta jihar Legas domin tabbatar da fito da hakikanin abubuwan da suka faru kan wannan danyen aikin.
“A karshen binciken, idan aka gano aka tabbatar wadanda ake zargi sojoji ne, za a kawosu gaban shari’a su fuskanci hukunci na soji da na dokar farar hula.
“A daidai lokacin da lamarin ke kan bincike, shalkwatar soji ta 81 na rokon iyalan mamacin su kasance masu hakuri su dan jira kadan zuwa fitowar sakamakon binciken za mu kuma tabbatar musu da adalci.
“Rundunar soji kwata-kwata ba ta lamuntar rashin da’a daga wajen jami’anta kuma kowani mutum aka samu da aikata ta’addanci dole ne ya fuskanci hukunci.
“A kan hakan, Kwamandan rundunar soji ta 81, Manjo Janar MT Usman, ya jajanta wa iyalan mamacin tare da yin alkawarin sanya ido wajen wanzar da adalci yadda ya dace.
“Ya tabbatar wa iyalan mamacin cewa ba za a taba barin ran da uwansu ya tafi haka nan ba tare da an hukunta makasan ba.”