Rundunar Sojin Nijeriya ta karrama jami’anta goma bisa kwazon da suka nuna a ayyukan rundunar daban-daban na yaki da ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane a sassan kasar.
Sojojin da suka kunshi maza biyar da mata biyar, an zabo su ne daga rundunoni shida na rundunar sojojin Nijeriya a yankin Kudu maso Yamma.
- Dokar Hana Fitar Da Kayan Gini Waje: Jami’an Tsaro Sun Kama Manyan Motoci 5 Makare Da Siminti A Adamawa
- ‘Yan Bindiga: Gwamna Dauda Ya Kai Ziyarar Jaje A Zurmi Da Birnin Magaji
Babban Hafsan Sojin kasa (COAS), Laftanar Janar Taoreed Lagbaja, ne ya bayar da lambobin yabo ga sojojin a wani taron karramawar da rundunar sojojin Nijeriya mai yaki da ‘yan ta’adda da kuma kwalejin kula da harkokin tsaro ta Nijeriya (NACOLM) suka saba shiryawa duk karshen shekara wanda aka gudanar a Legas.
Ya bukaci sojojin Nijeriya da su ci gaba da jajircewa tare da ci gaba da gudanar da ayyukansu wanda doka ta tanadar musu na kare martabar yankin Nijeriya.
Babban hafsan sojojin wanda ya samu wakilcin babban kwamandan runduna ta 81 (GOC), Janar Mohammed Usman, ya kuma umurci sojojin da su yi amfani da Kwarewar da suka samu wajen ci gaba da gudanar da ayyukansu na tsaron kasa.