Rundunar sojojin kasar Sin (PLA) ta ce tana ci gaba da kasancewa cikin shirin ko-ta-kwana, kuma a shirye take wajen kare cikakken ikon kasar na mallakar yankuna da tsaronta, da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin da kasar ke ciki.
Kakakin rundunar PLA, Shi Yi, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tsokaci kan ratsawar da jiragen ruwan yakin kasashen Canada da Australiya suka yi ta mashigin tekun Taiwan.
A cewar Shi Yi, a jiya Asabar, wani jirgin ruwan yakin kasar Canada mai suna Quebec, da kuma jirgin ruwan yakin kasar Australiya mai suna Brisbane, sun ratsa mashigin tekun Taiwan tare da yin tsokana, lamarin da ya aike da sakonni marasa dacewa da kuma kara hadari a fannin tsaro.
Ya ce a nasu bangare, sojojin ruwa da na sama na kasar Sin sun sa ido kan yadda jiragen ruwan yakin Canada da na Australiya suka bi ta mashigin tekun Taiwan tun daga farko har zuwa karshe, kuma sun mayar da kwararan martani da suka dace. (Bello Wang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp