Ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Rano-Bunkure daga Jihar Kano, Alhassan Rurum, ya buƙaci mutanensa da su daina zuwa Kudancin Nijeriya domin farauta.
Wannan na zuwa ne bayan da aka kashe wasu mafarauta a garin Uromi da ke Jihar Edo.
- Gwamnatin Sakkwato Ta Siyawa ‘Yan Gudun Hijira Gidan Miliyan 100
- UEFA: Wasan Arsenal Da Real Madrid Ya Haddasa Rikici A Tsakanin Magoya Bayan Kungiyoyin A Kano
Rurum ya yi wannan kira ne lokacin da ya kai ziyarar jaje ga iyalan waɗanda abin ya shafa a ƙauyen Bunkure a ranar Alhamis.
Ya ce matsalar rashin tsaro da ake fama da ita a faɗin ƙasar nan ta sanya ya zama dole a daina wasu ayyuka kamar farauta.
“Yan’uwanmu masu mafarauta su gane cewa lokaci ya sauya. Ba za ka ɗauki makamai irin su bindiga da adda ka tafi Kudu kana cewa za ka je farauta ba,” in ji shi.
Ya bayyana cewa shiga wani yanki da ba a fahimtar yaren juna ɗauke da makamai na iya janyo fargaba da tashin hankali.
“Ka yi tunanin idan wasu daga Kudu sun shigo ƙauyanku ɗauke da makamai kuma ba ku fahimtar yaren juna — za ku ji tsoro. Haka nan idan mutanenmu suka shiga yankin Kudu da makamai, su ma za a ji tsoro,” in ji shi.
Rurum ya ce zai gana da shugabannin ƙungiyoyin masu farauta a jihar domin daƙile wannan ɗabi’a, ya kuma buƙace su da su nemo hanyar nema wa kansu asiri .
“Wasu su tafi farauta su dawo ba tare da sun kamo ko ɓeran daji ba. Bai dace su ci gaba da haka ba. Ya kamata mu nemi wata hanya ta zaman lafiya da kwanciyar hankali,” in ji shi.
Haka kuma, ya bayar da gudunmawar naira miliyan biyar ga iyalan waɗanda suka rasu, sannan ya sha alwashin gina makaranta a garin domin girmama su.
Rurum ya kuma ce zai haɗa kai da Sanata Kawu Sumaila domin su kai ƙudiri a majalisa a kan kisan da aka yi wa mafarautan jihar a garin Uromi don ganin an yi wa waɗanda abin ya shafa adalci.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp