Biyo bayan rushewar wani gini mai hawa biyu a kan babban hanyar layin Legas da ke gundumar Garki II a Abuja wajajen karfe 11:45 na daren ranar Laraba, ministan birnin tarayya, Nyesom Wike, ya bada umarnin a gaggauta kamo wanda ya mallaki ginin da ya rushe din.Â
Wike, wanda ya bada umarnin a lokacin da ya ziyarci wurin da lamarin ya faru da safiyar ranar Alhamis, ya jinjina da aikin ceto da aka ake yi a ginin, ya kuma ce, rushewar ginin abun takaici ne da suka wayi gari da shi.
- FIFA Ta Fara Bincike Kan Sumbata Da Rubiales Ya Yi Wa ‘Yar Wasan Spain
- Xi Jinping: Za Kara Karfin Wanzar Da Zaman Lafiya Da Ci Gaban Duniya
Ya ce: “Ba abun da muka tsammaci faruwarsa ba ne. Bar na yaba wa hukumomi, musamman NEMA da FEMA bisa kasancewa da suka yi a nan domin taimakonmu wajen ceton rayuwa a kalla 32. Abun bakin ciki da takaici mun rasa mutum biyu daga cikinsu.
“Ina fatan babban sakatare zai tabbatar an samar da kudaden da za a biya jinyar wadanda aka ceto, don kar mu sake rasa wani mutum kuma, sannan, wannan zai faru ne cikin gaggawa.
“Na biyu, wadannan abubuwan ne fa muke ta fada, ba wanda ya san hakan zai faru, kazalika, lokacin da gwamnati ta ce za ta dauki mataki kan gine-ginen da aka yi ba bisa ka’ida ba, ba za a yi hakan don wani mutum daya ko don ni ba ne, a’a za a yi ne don mu dukka kuma don komai su tafi daidai,” ya shaida.
Ministan FCT din ya nuna bacin ransa kan yadda hukumar kula da birnin tarayya (FCTA) ta dauki tsawon lokaci ba tare da ta zauna da mazauna kauyen Garki ba, ya ce, cikin gaggawa ya na son a zauna da mutanen kauyen domin fito musu da tsarin da gwamnati take son yi a wannan yankin.
“Idan gwamnati ta ce ga tsarin gini kaza da take son a yi, ba wai don a musguna ma wani ba ne, sam, illa domin a kare lafiyar kowa da kowa ne. An shirya birane domin dakile faruwar irin wannan. Abun takaici ka ga gine-gine ba tare da amincewar yin ginin ba. Na umarci a nemo tare kamo mamallakin wannan gini. Ya na da matukar muhimmanci.
“Babu shakka gwamnati za ta amshi ragamar wannan yankin kuma a tabbatar ba abun da ya sake faruwa. Ina rokon dukkanin mutanen wannan yankin da su ba mu hadin kai domin kyautata rayuwar kowa. Babu wanda ya zo nan domin ya ce ina son wane, ba na son wa ne.”
Daga karshe dai ya jajanta ma iyalan wadanda suka rasa rayukansu tare da addu’ar Allah zai bai wa wadanda suka jikkata lafiya.
Shi ma da yake jawabi, daraktan sanya ido kan harkokin bunkasawa ta hukumar FCTA, Muktar Galadima, ya ce za su cigaba da sanya ido domin tabbatar da jama’a su tashi a wuraren da ba amince a yi gini a cikinsu ba musamman wuraren da suke kan hanyar ruwa.