A kalla mutane bakwai ne suka rigamu gidan gaskiya a sakamakon barnar da ambaliyar ruwa ta yi a sassan daban-daban na jihar Kwara a wannan shekarar.
Kusan kowace shekara dai sai an samu ambaliyar ruwa a kogunan da ke kauyukan karamar hukumar Patigi.
Adadin gidaje 1,300 da mutane 2,800 ne ambaliyar ta shafa tare da lalata gonaki daban-daban a Patigi.
Manajan gudanarwa na HYPPADEC, Alhaji Abubakar Yelwa, shi ne ya shaida hakan a ranar Lahadi a Patigi da ke jihar Kwara.
Yelwa wadda ke bayanin lokacin da ya kaddamar da raba kayan tallafin rage radadin da ya kai na miliyan 50 ga wadanda ambaliyar ta shafa a jihar.
Daga cikin kayayyakin tallafin da ya rabar har da kayan abinci buhu 500, katon-katon na sabulu, Katifu 1,300, sinadarin wanki da sauran kayan amfanin yau da kullum.
Da yake nasa jawabin, Mahmud Muhammed, Yelwa ya gargadi wadanda suke rayuwa a kusa da kuguna da su tashi domin kiyaye kawukansu daga ambaliyar.
Daya daga cikin wadanda suka amfana da tallafin, Mohammed Garba, ya ce ya rasa gonarsa da amfanin gonar na shinkafa da ya zarce kadada 1, ya nuna damuwarsa kan halin da suke ciki.