Sabon Gwamnan Jihar Sakkwato, Ahmed Aliyu ya bayyana cewar a bisa ga burin da yake da shi na bunkasa Jihar Sakkwato, yana kira ga wadanda basu samu nasara a zabe ba da su baiwa gwamnatinsa goyon baya domin raya Jihar.
Aliyu ya bayyana hakan a yau Litinin bayan da Babban Mai Shari’a na Jihar Sakkwato, Muhammad Sa’idu Sifawa, ya rantsar da shi a matsayin gwamna bayan rantsar da Mataimakinsa, Idris Muhammad Gobir.
- Kotun Sauraren Karar Zabe Ta Kaddamar Da Zama A Sakkwato
- Majalisar Dokoki Ta Amince Da Dokar Kayyade Tsadar Aure A Sakkwato
Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatinsa ta kowa da kowa ce, don haka za su baiwa marada kunya wajen sauke nauyin da aka dora masu tare da neman shawarwari domin samun nasara.
“Gwamnatin mu za ta ci gaba da bayar da fifiiko da karfafawa matasa a fannin sha’anin tsaro da tsaftar muhalli da samar da ruwan sha da bunkasa ilimi da tattalin arziki. Za mu yi hakan ne domin cika alkawurran da muka yi na dawo da martabar Jihar Sakkwato.