Sabon jakadan kasar Sin a Amurka Xie Feng, ya bukaci Amurka da ta yi aiki tare da kasar Sin, wajen inganta tattaunawa, hadin gwiwa da daidaita bambance-bambance, ta yadda za a iya dawo da hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu kan hanyar da ta dace.
Xie ya bayyana a takaitaccen jawabinsa ga manema labarai, lokacin da ya isa filin jirgin sama na John F. Kennedy a yammacin jiya Talata cewa, ya yi matukar farin ciki da shugaba Xi Jinping ya nada ni a matsayin jakadan kasar Sin a kasar Amurka na goma sha biyu.
Ya ce, a halin yanzu, dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka tana fuskantar matsaloli da kalubale masu tsanani, nadin sa kan wannan mukami, ba wai girmamawa kadai yake nufi ba, har ma da nauyi mai girma, shi da abokan aikinsa, za su gudanar da ayyukansu cikin himma da kwazo yadda ya kamata.
Xie ya ce, shugaba Xi ya gabatar da ka’idoji guda uku na mutunta juna, da zaman lafiya, da hadin gwiwar samun nasara tare, wadanda ke wakiltar muhimmiyar hanyar da ta dace da kasashen biyu su yi mu’amala da juna a sabon zamani. (Mai fassarawa: Ibrahim)