A yau Lahadi ne aka bude layin dogo da ya hada biranen Lijiang da Shangri-la, fitattun wuraren shakatawa a lardin Yunnan na kudu masa yammacin kasar Sin, a cewar hukumomin kasar.
Da fara aikin wannan layin dogo na Lijiang da Shangri-la, tsawon lokacin zirga-zirga mafi sauri tsakanin biranen biyu zai kasance awa 1 da mintuna 18.
- Kasar Sin Ta Bukaci Japan Ta Amince Kasashen Duniya Su Sa Ido Kan Yadda Take Zubar Da Ruwan Dagwalon Nukiliya Cikin Teku
- Shugaban Uruguay: Shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya Ta Kawo Sabuwar Dama Ga Hadin Gwiwar Dake Tsakanin Uruguay Da Sin
Hari la yau, layin dogon mai nisan kilomita 139 ya hada Shangri-la, da ke yankin Diqing mai cin gashin kansa na lardin Yunnan, da Kumming, babban birnin lardin.
Sabon layin dogon zai taimaka wajen inganta harkokin sufuri a yankunan da aka fi samun mabambantan kabilu, wanda zai sa kaimi ga hadin kan kasa, da tabbatar da zaman lafiyar kan iyakoki, da kuma sa kaimi ga bunkasuwar lardin Yunnan, a cewar babban kamfanin jirgin kasa na kasar Sin. (Yahaya)