• English
  • Business News
Sunday, July 27, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sabon Shirin Kasar Sin Zai Taimakawa Raya Masana’antu A Afirka

by CGTN Hausa
1 year ago
in Ra'ayi Riga
0
Sabon Shirin Kasar Sin Zai Taimakawa Raya Masana’antu A Afirka
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

A wajen wani taron da shugabannin kasar Sin suka kira a kwanan baya, dangane da aikin raya tattalin arziki, an jaddada muhimmancin manufar raya sabon karfin samar da bunkasuwa. Makasudin wannan manufa shi ne sa kaimi ga kokarin kirkiro sabbin fasahohi, daga baya a yi amfani da fasahohin da aka samar wajen raya masana’antu. Kana manufar ta kunshi fannonin da suka hada da inganta tsoffin masana’antu ta hanyar fasahar zamani, da raya sabon makamashi, da harkar sadarwa, da sauran sabbin ayyukan masana’antu. Gami da raya masana’antun da za su samar da amfani a nan gaba, kamar masu alaka da na’ura mai kwakwalwa ta kwamfuta irin na Quantum, da fasahar sadarwa ta 6G, da dai sauransu, da kuma horar da kwararrun ma’aikata da za su iya sarrafa sabbin fasahohi.

A ganina, wannan manufa ta kasar Sin za ta samar da dama mai muhimmanci ta raya masana’antu a nahiyar Afirka.

  • Shugaban Kasar Saliyo Zai Kawo Ziyara A Kasar Sin
  • ‘Yansanda Sun Kama Mutum 3 Kan Zargin Tayar Da Hargitsi A Kasuwar ‘Yan Magani Ta Kano

To, ko me ya sa nake iya tabbatar da haka? Saboda da farko, kasar Sin mai goyon bayan kasashen Afirka ce a fannin raya masana’antu.

Kasar Sin ta kwashe shekaru fiye da 100 tana kokarin raya bangaren masana’antunta, inda ta sha wahalhalu da matsin lamba iri daya da wadanda kasashen Afirka ke fama da su. Kana bisa kokarin nema, kasar ta samu dabarar bunkasa masana’antu mai dacewa. Saboda haka, dangane da mawuyacin halin da kasashe masu raunin tattalin arziki suke ciki ta fuskar raya masana’antu, kasar Sin tana da wani ra’ayi da ya sha bamban da na kasashen yamma, inda kasar Sin ta kan jaddada muhimmancin raya tattalin arziki da inganta bangaren masana’antu a kasashe masu tasowa. Kana yayin da kasar ke neman raya masana’antunta, tana kuma fatan ganin kasashen Afirka sun samu ci gaba na bai daya, da kawo karshen yanayin koma bayan tattalin arziki, da sarrafawa da cin zarafi da kasashen yamma ke yi musu.

Na biyu shi ne, sabanin yadda kasashen yamma ke kallon tsarinsu a matsayin wanda ya fi kyau a duniya, da yadda suke son ba da umarni ga kasashen Afirka, kasar Sin ta kan samar da dabarar raya masana’antu da ta dace da hakikanin yanayin da kasashen Afirka suke ciki.

Labarai Masu Nasaba

Bai Kamata a Rika Kai wa Fararen Hula Hari Ba!

Tursasawa Kasashen Afirka Karbar Bakin Haure Daga Amerika Kuskure Ne

Misali, ta la’akari da yadda ake fama da karancin tsare-tsaren da za su taimakawa raya masana’antu, da rashin isassun hanyoyin jigilar kayayyaki a Afirka, kasar Sin ta dauki wasu matakai 3 yayin da take aiwatar da ayyukan hadin gwiwa na raya masana’antu a kasashen Afirka: Da farko ta gina dimbin yankunan masana’antu don tabbatar da gudanar ayyukan manyan ma’aikatu yadda ake bukata. Kana na biyu shi ne, kasar Sin da kasashen Afirka sun kirkiro ayyukan masana’antu masu alaka da kayayyakin more rayuwa da aka gina, don tabbatar da cewa kudin da aka kashe wajen gina kayayyakin more rayuwa na samar da amfani da riba. Yayin da na 3 shi ne, kasar Sin na dora muhimmanci kan zuba jari ga masana’antun samar da kayayyakin da ake bukatarsu a kasuwannin kasashen Afirka, lamarin da ya ingiza tsarin raya masana’antu na kasashen Afirka na mai da hankali kan kasuwannin cikin gida, ta yadda ake tabbatar da ci gaban aikin raya bangaren masana’antu a kai a kai.

Ban da haka, dalili na karshe da ya sa nake sa ran ganin amfanin manufar kasar Sin kan raya masana’antu a Afirka shi ne, kasar ta dade tana samar da fasahohin samun ci gaba ga kasashen Afirka, don ciyar da tattalin arzikinsu gaba ta wata ingatacciyar hanya.

Misali, a shekarun baya, karin kasashen dake nahiyar Afirka sun mai da tattalin arziki mai alaka da fasahohin zamani a matsayin sabuwar dabarar neman samun ci gaba, bisa hadin gwiwa da kasar Sin. A kasashen da suka hada da Najeriya da Kenya, da dai sauransu, dandalin biyan kudi ta wayar salula da kamfanoni masu jarin kasar Sin suka kafa na samar da dabarar biyan kudi mai tsaro da sauki ga mutane fiye da miliyan 10. A sa’i daya, kamfanonin kasar Sin sun kaddamar da ayyukan horar da kwararru na fannonin fasahar sadarwa, da ciniki ta yanar gizo ko Internet a kasashen Afirka, inda aka ba dimbin matasan nahiyar Afirka damammaki na koyon fasahohi masu inganci, da wadanda suka shafi kafawa da kula da kamfanoni, ta yadda za a taimakawa kasashen Afirka a fannin zamanantar da fasahohi.

Ta wadannan abubuwa da na bayyana za mu san cewa, kasar Sin na son taimakon kasashen Afirka wajen raya masana’antu, kuma ta san dabara mai dacewa da ya kamata a dauka don taimakawa. Ban da haka, kasar ta dade tana raba fasahohinta masu inganci ga kasashen Afirka, don neman samun ci gaban tattalin arzikinsu na bai daya. Saboda haka, kokarin kasar Sin na raya sabbin fasahohi da sabbin nau’ikan masana’antu tabbas zai samar da damammaki masu kyau na raya tattalin arziki ga kasashen Afirka.

Na kan ji yadda abokaina na Najeriya suke fadin cewa, “A lokacin da kasar Sin ta hau duniyar wata, to, ta tafi tare da Najeriya. ” To, idan kun yarda, zan so in gyara maganar, sa’an nan in sanya ta a karshen wannan sharhi, wato: Lokacin da Sin ta hau duniyar wata, tabbas za a samu kasashen Afirka a can, tare da kasar Sin. (Bello Wang)


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Majalisar Zamfara Ta Dakatar Da Mambobi 8 Tare Da Rusa Kwamitocinta

Next Post

Gobara Ta Kone Shaguna 50 A Kasuwar ‘Yan Katako A Kano

Related

Bai Kamata a Rika Kai wa Fararen Hula Hari Ba!
Ra'ayi Riga

Bai Kamata a Rika Kai wa Fararen Hula Hari Ba!

4 days ago
Tursasawa Kasashen Afirka Karbar Bakin Haure Daga Amerika Kuskure Ne
Ra'ayi Riga

Tursasawa Kasashen Afirka Karbar Bakin Haure Daga Amerika Kuskure Ne

4 days ago
Wace Kasa Ce Take Son Zama “Kasa Ta Uku Mai Tsaro” A Wurin Amurka?
Ra'ayi Riga

Wace Kasa Ce Take Son Zama “Kasa Ta Uku Mai Tsaro” A Wurin Amurka?

1 week ago
Lai Ching-Te Bai Cancanci Zama Jagoran Yankin Taiwan Ba
Ra'ayi Riga

Lai Ching-Te Bai Cancanci Zama Jagoran Yankin Taiwan Ba

1 week ago
Manufar Raya Biranen Kasar Sin: Ba Wai Kawai a Tabbatar Da “Tsayi” Ba Ne Har Ma Da “Zafi”
Ra'ayi Riga

Manufar Raya Biranen Kasar Sin: Ba Wai Kawai a Tabbatar Da “Tsayi” Ba Ne Har Ma Da “Zafi”

1 week ago
Girman Kai Da Son Zuciya Ba Za Su Sa A Amince Ko Ba Da Hadin Kai Ba
Ra'ayi Riga

Girman Kai Da Son Zuciya Ba Za Su Sa A Amince Ko Ba Da Hadin Kai Ba

2 weeks ago
Next Post
Hukumar kashe gobara

Gobara Ta Kone Shaguna 50 A Kasuwar 'Yan Katako A Kano

LABARAI MASU NASABA

Shanghai Ya Gabatar Da Shirin Gina Yankin Motoci Masu Tuka Kansu

Shanghai Ya Gabatar Da Shirin Gina Yankin Motoci Masu Tuka Kansu

July 27, 2025
Sin: Fasahar Rage Asarar Hatsi Ta Yi Amfani

Sin: Fasahar Rage Asarar Hatsi Ta Yi Amfani

July 27, 2025
‘Yansanda Sun Cafke Wasu Sojojin Bogi 2 A Legas

‘Yansanda Sun Kashe ‘Yanbindiga Uku Da Kama AK-47 Guda Goma

July 27, 2025
Shetima Zai Wakilci Nijeriya A Taron Tsarin Abinci A Addis Ababa

Shetima Zai Wakilci Nijeriya A Taron Tsarin Abinci A Addis Ababa

July 27, 2025
Gwamnati Ta Ba Da Wa’adin Mako 6 Don Kammala Ginin Rukunin Gidaje A Kano

Gwamnati Ta Ba Da Wa’adin Mako 6 Don Kammala Ginin Rukunin Gidaje A Kano

July 27, 2025
Super Falcons Za Su Samu Kyakkyawar Tarɓa Daga Gare Ni A Abuja — Tinubu

Super Falcons Za Su Samu Kyakkyawar Tarɓa Daga Gare Ni A Abuja — Tinubu

July 27, 2025
ADC Ce Za Ta Haɗa Kan Arewa Wajen Kawo Ci Gaba — Mark

ADC Ce Za Ta Haɗa Kan Arewa Wajen Kawo Ci Gaba — Mark

July 27, 2025
Hanyoyin Da Za A Bi A Rage Yawan Zawarawa

Hanyoyin Da Za A Bi A Rage Yawan Zawarawa

July 27, 2025
Ƴansanda Sun Kama Masu Garkuwa Da Mutane 6 A Kaduna Da Zamfara

Ƴansanda Sun Kama Masu Garkuwa Da Mutane 6 A Kaduna Da Zamfara

July 27, 2025
aure

Ko Kin San… Matsalolin Mahaifa Da Suke Hana Haihuwa 

July 27, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.