A halin yanzu bangaren masana’antun albarkatun man fetur na Nijeriya na fuskantar barazana sakamakon janye jarin da ya kai na Dala Biliyan 21 da manyan kamfanonin mai na duniya suka yi a ‘yan tsakanin nan, wanda hakan ya kai ga tabarbarewar al’amurra a bangaren da kuma barazana ga tattalin arzikin kasa.
Hukumar daidaita farashin albarkatun man fetur (NUPRC) ta dora alhakin yadda aka janye jarin a kan yadda aka shiga zullumi kafin zartar da dokar alkinta albarkatun man fetur na (PIA) a shekarar 2021, da kuma sauye-sauyen da aka fuskanta a bangaren albarkatun man fetur a yayin da duniya ta kamu da annobar cutar korona.
Wani rahoto ya nuna cewa, an samu raguwar fiye da kashi 70 na kudaden da aka zaba jari a bangaren hako albarkatun mai na cikin teku a cikin shrekara 8 da suka wuce.
Yanayin jarin da aka zuba a bangaren albarkatun man fetur a duk shekara ya yi kasa da biliyan 27 a sherkarar 2014 zuwa kasa da Dala Biliyan 6 a shekarar 2022. Sanannun masu zuba jari a harakar albarkatun man fetur kamar Shell, EddonMobil, Total, Chebron, da Eni sun dade suna janye jarinsu daga Nijeriya ta hanyoyi daban-daban tun daga shekarar 2010.
Nijeriya ta matukar dogara ga kudade shiga daga albarkatun man fetur, bangare mai tsoka na kasafin kudin Nijeriya daga kudaden da ake fitowa daga albarkatun man fetur suke fitowa.
Wannan janye jarin na matukar barazana ga ginshikin hanyar shigar kudaden Nijeriya, wanda haka ke kaiwa ga samar da gibi a kasafin kudin kasa, rage kashe kudade a kan al’amurran da suka shafi al’umma da kuma rashin tabbas a bangaren tattalin Nijeriya. Wannan lamarin ya kara haifar wa da Nijeriya babbar matsala musamman ganin farashin albarkatun mai a kasuwannin duniya bashi da tabbas.
Wannan janyewar zuba jarin na iya haifar da mastala ga bangaren ma’aikatan Nijeriya. Bangaren albarkatun man fetur na daya daga cikin bangaren da ke daukar ma’aikata da dama a Nijeriya, haka kuma bangaren na taimakawa wajen samar da aikin yi kai tsaye da kuma a kaikaice ga al’ummar Nijeriya da dama, wanda hakan yana nuna cewa za a samu rasa aikin yi mai yawa sakamakon janye jarin da manyan kamfanonin kasashen waje ke yi, wanda kuma hakan zai matukar shafar harkokin rayuwar al’umma na yau da kullum zai kuma taimaka wajen kara talauci da tashe-tashen hankula a tsakanin al’umma.
Wannan janye jarin da aka samu ya haifar da babbar gibi a bangaren samar da aikin yi a kamfanonin albarkatun man fetur na Nijeriya. A bayyane yake cewa, wadannan kamfanonin ke da kudade da kwarewar da ake bukata na hakar man fetur din a tudu da cikiin teku sune kuma suke da dukkan abin da ake bukata na tabbatar da ci gaba da aikin hakar man fetur da abin da ya shafi sarrafa albarkatun man fetur gaba daya.
A kan haka wannan janyewar zuba jarin zai iya kawo cikas ga dukkan kokarin Nijeriya na hako da sarrafa albakatun man fetur don ci gaba al’umma da bunkasar tattalin arzikin kasa.
An dade ana zargin kamfanonin mai na kasa sasboda yadda suke haifar da matsaloli ga muhalli, abubuwna da suka hada da haifar da gurbacewar muhalli, zubar da man fetur da sauran matsaloli ga muhalli.
Wannan janyewar jari da aka fuskanta zai kawo cikas ga matakan da ake dauka don takaita barnar da harkokin yake haifarwa ga muhalli. Hakan kuma zai iya tsawaita shirin samar da cilkakkiyar kiwon lafiya ga al’ummar da ake hako man fetur din da kuma shirin kasa da kasa na kawo karshen zaizayar kasa da abubuwan da ke cutar da muhalli.
Domin maganin matsalolin da janye zuba jari a bangaren masana’antun man fetur ka iya haifarwa ga Nijeriya ya kamata a dauki wadannan matakan:
A nasa shawarar wani Malami a Jami’a Jihar Nasarawa, Dauda Ibrahim, ya bayyana cewa, dole Nijeriya ta gaggauta samar da wasu hanyoyin samun kudaden shiga baya ga na bangaren albarkatun man fetur. Bunkasa wasu bangarori kamar aikin noma, kimiyya da fasaha da kuma rage dogaro ga kudaden da ake samu daga bangaren albarkatun man fetur ta yadda za a iya samar da aikin yi ga matasa.
“Dole gwamnatin ta gagguta aiwatar da tsare tsaren shirin nan na saukaka hanyoyin gudanar da harkokin kasuwanci a cikin al’umma, su kuma jawo masu zuba jari da kuma samar da yanayi mai kyau ga kamfanonin ciki da wajen Nijeriya ta yadda za su gudanar da harkokin kasuwancinsu.
Wannan kuma ya hada da ganin an rage matsalolin da hukumomin da ke sanya ido a harkokin masu zuba ke yi da kuma samar da abubuwan da za su janyo hankalin masu son zuba jari a cikin kasa, musamman masu son zuba jari a bangaren albarkatun man fetur.
“Karfafa bunkasar kamfanonin gida da kuma karfafa sanya baki daga al’umma gida don suma sun san ana yi da su, ana iya cima wannan ta hanyar samar da dokoki masu sauki da kuma samar musu da basuka marasa ruwa masu yawa,” in ji shi.
A nasa gudummawar, manaja a kamfanin Cashlinks Ltd, Festus Soludo, ya bayyana cewa, “Janye jarin Dala Biliyan 21 da manyan kamfanonin duniya suka yi ya kara karfafa barazanar da tattalin arzikin Nijeriya ne fuskanta. Hakan kuma ya kara karfafa bukatar samar da wasu hanyoyi na daban ga Nijeriya don tafi da harkokn tattalin arzikinta, dole a san hanyoyin kara janyo sabbin masu zuba jari da kuma samar da sabbin hanyoyin tafiyar da bangaren albarkarun man fetur na kasa, in har za a bi wadanna shawarar Nijeriya na iya tsallake wannan barazanar har kuma a kai ga tudun mun tsira, a samar da karkarfar tattalin arziki da duk wani dan Nijeriya zai iya alhafari da shi.
Haka kuma, a nasa tsokacin, wani malamin jami’a, a Jami’ar Jihar Ebonyi, Dakta Nelson Nkwo, ya bayyana cewa, in har ana son a kauce wa matsalolin da janye wadannan jarin da kamfanonin kasashe waje suka yi zai haifar, dole Nijeriya ta gaggauta zakulo wasu hanyoyin dogaro ga tattalin arzikinta koma bayan bangaren albarkatun man fetur.
Ya ce wadannan hanyoyin kuma sun hada da aikin gona, masa’anantu, kimiyya da fasaha da kuma samar da sabbin guraben ayyukan yi ga matasanmu.’