Al ‘ummar yankin Karamar Hukumar Nafada a Jihar Gombe, na fuskantar barazana sakamakon bullar wata cuta da ta lakume rayukan yara da matasa sama da 30.
Cutar wadda ta fara kunno kai a cikin farkon watan Fabrairu, tana da alamun zazzabi da ciwon ciki, da ciwon kafa da kuma amai kamar yadda bincike ya nuna.
- NiMet Ta Yi Hasashen Bullar Zazzabin Cizon Sauro A Watan Maris Da Afrilu
- An Kama ‘Yan Sintiri 10 Kan Zargin Kashe Limamin Garin Mada
Bayanai daga babban asibitin garin Nafada, ya nuna cewar an kai samfurin cutar guda 20 kuma sakamakon mutane 11 ya nuna cewar ba cutar sankarau ba ce kamar yadda ake hasashe da farko.
Haka zalika, bisa bayanan da suke da shi akwai mutane guda bakwai da suka rasu, sauran mace-macen da basa da kididdigarsu sun faru ne a cikin gari.
Sakataren Gudanarwa na Babban Asibitin garin Nafada, Mista Kefas K. Silanda, ya yi karin bayani da kuma tabbatar da yanayın cutar, adadin wadanda suka mutu a asibitin da matakan da likitoci suka dauka na gwajin samfurin cutar.
A baya-bayan nan dai cutar sankarau ta bulla a jihar, lamarin da ya yi sanadin kwantar da mutane da dama.