Kasar Sin ta wallafa shirin “Dabarun inganta daidaiton kayayyakin saye da sayarwa don kara habaka ciniki”. Game da hakan, kafofin watsa labaru na kasa da kasa sun fadi ra’ayoyinsu. Rahotanni sun nuna cewa, a yayin da ci gaban tattalin arzikin duniya ya nuna sanyin jiki, wannan takardar ita ce ta farko da aka fitar tun bayan cikakken zama na 4 na kwamitin tsakiyar JKS na 20, kuma za ta kawo sabbin damammaki ga dukkan bangarori.
A halin yanzu, tattalin arzikin kasar Sin ya kusa kaiwa mataki na ingantaccen ci gaba. Manufar shirin ita ce sanya masu samar da hajoji su dace da sabbin sauye-sauyen yanayin ciniki. Hakazalika, hakan zai baiwa kamfanoni jagorancin bin hanya da ta dace don samar da kayayyaki da za su biya bukatu, da samar da kayayyaki masu inganci, da kuma farashi mai kyau, don cimma kyakkyawar mu’amala tsakanin masu saye da masu sayarwa, wanda zai kara karfafa karfin ciniki, kuma ya taimaka wajen ingantacciyar farfadowar tattalin arziki.
A matsayinta na kasa ta biyu mafi girman kasuwar ciniki a duniya, sabuwar manufar ciniki da kasar Sin ta kaddamar babu shakka ta dace da duniya baki daya, saboda za ta kara fadada babbar kasuwar kasar Sin, kuma za ta samar da damammaki masu yawa na cin nasara tsakanin kasa da kasa.
Kirkire-kirkire su ne mabudin ingiza ciniki gaba. Shirin ya ba da shawarar yada sabbin fasahohi da sabbin hanyoyi, gami da kara kaddamar da sabbin fage da sabbin hanyoyin gasa, da kuma karfafa amfani da fasahar AI, wanda hakan zai baiwa duniya, musamman ma kamfanonin kasashen waje, damar samun sabbin kirkire-kirkire.
Bukatun cinikin Sinawa na karuwa kullum, wanda ke bukatar ingantattun kayayyaki, da kuma wadatar hanyoyin saye. Kadara da aiwatar da sabuwar manufar ciniki ta kasar Sin, ba wai kawai za ta kara gamsar da bukatun al’ummar Sinawa ta rayuwa mai kyau ba ne, har ma hakan zai baiwa sassan kasa da kasa damar fahimtar darajar “Sayayya a kasar Sin” da kuma muhimmancin “Zuba jari a kasar Sin.” (Amina Xu)














