Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun, ya taya al’ummar Musulmi murnar shigowar sabuwar kalandar Musulunci ta 1444 bayan Hijrah.
Abiodun a cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaransa, Kunle Somorin, ya fitar a jiya, ya ce sabuwar shekarar Musulunci tana wakiltar sabunta ruhi wanda ya samo asali daga hijirar Fiyayyen Halitta, Annabi Muhammad (SWT) ya yi daga Makka zuwa Madina.
- Kotu Ta Sa A Yi Wa Matashi Bulala 12 Saboda Samunsa Da Kayan Maye
- Shin Wane Ne Ya Danawa Kasashen Afrika “Tarkon Bashi”?
Ya kara da cewa, yayin da al’ummar musulmi a duk fadin duniya suke bikin sabuwar shekara, dole ne a himmatu wajen ganin an kwadaita da kyawawan halayen Annabi, ta hanyar nuna soyayya, zaman lafiya da hadin kai.
Da yake taya al’ummar Musulmin jihar murna, Abiodun ya bukace su da su yi amfani da wannan dama don yin addu’a ga kasa baki daya da kuma jihar Ogun.
Don haka ya jaddada aniyar gwamnatinsa na samar da zaman lafiya da hadin kai tsakanin addinai da kuma ci gaba da kokarin ganin an samar da shugabanci nagari a fadin jihar.