Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya aika da saƙon taya murnar shiga sabuwar shekarar musulunci ta 1446H ga al’ummar jihar.
Cikin saƙon da ya aika wa al’ummar, Gwamna Lawal ya yi fatan wannan sabuwar shekara za ta zama mai cike da albarka ga al’ummar jihar da ma ƙasa baki ɗaya, inda ya hore su da su zama masu jajircewa cikin addu’o’in neman dawowar dawwamammen zaman lafiya.
A cikin wata sanarwa da Kakakin Gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya sanya wa hannu, ya bayyana cewa wannan sabuwar shekara ta zama wani lokaci na tilawar abubuwan da suka gudana a shekarar da ta gabata, don dunfarar ci gaba a wannan sabuwar shekara.
“Yau ɗaya ga watan Muharram, wanda ya kawo ƙarshen shekarar 1445H, kuma ita ce farkon shekarar musulunci ta 1446H.
“Wannan wata dama ce, ba ga al’ummar jihar Zamfara kawai ba, dama ce ga dukkan al’ummar ƙasar nan wajen dagewa da yin addu’o’i don samun zaman lafiya.
“Dukkan mu muna da muhimmin rawan da za mu take wajen ci gaban jihar mu da ƙasa baki ɗaya.
“Ina yi wa jama’a fatan alhairi da ci gaba mai amfani mara iyaka. Allah kare mana jihar mu ta Zamfara da Nijeriya baki ɗaya.