Assalamu Alaikum Wa Rahmatullahi Ta’ala Wa Barakatuhu.
Da farko kafin na fara cewa komai ina mai jajanta wa al’ummar Nijeriya musamman jahohin Arewa bisa iftila’i na zanga-zanga, domin dole mu kira shi da iftila’i. A ka’ida ta doka babu inda aka hana dan kasa yayi zanga-zangarsa, matsalar da take faruwa wajen yin zanga-zangar wasu batagari sun yi abubuwan da bai kamata ba na sace-sace da dibar kayan mutane.
Kullum Kuka muke na cewar; shuwagabanni ba sa yi mana adalci a wajen shugabancin da suke yi, tunda zabarsu muka yi su yi mana abin da ya dace to, kuma kana kukan cewa kai ka zabi shugaba bai yi maka adalci ba, shugaba baraho ne, kuma kai ka je kana satar kayan wani to, kai da shugaban wane ne barawon?
Wannan kuskure ne, kullum idan har za ka rika biyewa son zuciya muna yarda da irin wannan abun na biyewa son zuciyar mu, haka za mu wayi gari kasar ma ba ta gyaru ba.
Ni a iya tunani na za mu yi wa kanmu fada ne a kan irin wadannan abubuwa da suke faruwa na cewar ina ne sauki, idan Allah bai kawo muku sauki ba babu wanda ya isa ya kawo mana sauki. Na farko mu yi addu’a, domin zagin shugabannin da muke ba fasikanci ba kuskure ne, Allah ya fada duk mutumin daya zalunce ka kana yunkurin neman sakayyarka gurin ubangiji Allah zai saka maka. Na yi imani idan da duk shugaban daya zalunce mu ya zo lokacin zabe muka yi abin da ya dace, wajen zabar ma wanda ya dace muka zaba, da duk ba mu rika fuskantar kanmu a irin wannan kuskuren ba.
A takaice iyaye na gida ‘ya’yanku maza ko mata ku dakatar da su a kan irin abubuwan da suke faruwa, dole ne ka ja kunne a kan danka ya shigo maka da buhun Shinkafa ko katan din Taliya, ko ya zo yana murma wani ya samo galan din mai, idan har ka goyawa danka baya a irin wannan to, a irin haka ne ake fita a harbe danka ba tare da ka’ida ba. Za a yi ta harbe muku ‘ya’ya idan har baku dauki mataki ba, dole ka tsaya ka tsaida gidanka, zanga-zanga ba a hanata ba amma ta lumana ba ta sace-sace da fasa kayan mutane ba.
Idan kana murna an fasawa wani shago to, ka sani cewar fa kai kuma kana sake murna ne barayi suna kara karuwa a cikinku, dole ne a dakatar. Ina mai bayar da shawara ga kowa idan a kan layi ne kowa a layinsu ya hana dan wani layin ya shigo ya ce zai yi musu wani abu ba daidai ba, a haka–haka idan kowane layi zai dakatar da cewa kowa yayi abinsa a cikin layinsu to, ai ba wanda zai isa yayi sata a layinsu. idan irin wannan za a yi dole ne shuganni su tsaya su kalli mutane su ga me ya kamata ayi?,.
Sannan a gaba ta siyasa ita kuma idan har shugaban kasa sakona ya je gare shi, ina mai bashi shawara da wadannan kudi da ake cewa ana bawa gwamnoni da kayan abinci su rabawa mutane to, dan Allah a canja salo, saboda sako baya zuwa ga talaka domin talakan na kukan cewar; su ba su ma san wannan ana yi ba, a canja salo.
Ko dai a saka musu sauki ta wani bangaren da suke da bukata ko kuma dai a san ya za a yi sakon ya rika zuwa gare su.
A mahanga nan gaba shugaban kasa da wasu shugabannin cewar tainuwa fa biyu suke nema su yi ko tainuwa daya ba a yi ba shekara daya aka yi da wasu watanni, kuma nan gaba kadan za su sake dawowa cikin al’umma neman goyon bayansu su kuma zabarsu a wasu kujerun, to, ni ina mai bayar da shawara shuwagabannin mu ku kalli meye mafita?,
me ya sa ake yin zanga-zangar nan?,
meye za a yi kowa ya koma gida yayi harkokinsa, ana neman sauki a cikin rayuwar?, a’a! tallafin man ne jama’a suke ganin cewar idan ‘Subsidy’ nan ya kamata a sake dawo da shi ko na dan lokaci ne?,
Al’umma su sani, shugabanni su sani kashe su ake yi.
Malamai ku kuma addu’a ya kamata ku yi kune malamai ku ne jagorori addu’a ya kamata ku yi, ba magana ta siyasa ba, su ma kuma ‘yansiyasa kuskure ne ka rika fadar magana a cikin siyasa ka yi abin da za a kawo jahohi da kasa zaman lafiya domin yin maganganun siyasar ma zai iya tada wani tunzurin, ina mai kira da addu’a da mutane, masallatai da kowane lokaci idan aka yi sallah khamsu salawat sallolin nan guda biyar da mu yi addu’a Ubangiji Allah ya kaho mana sauki, duk shugaban da ba alkhairi bane Allah ya gaggauta dauke mana shi ya kaho mana alkhairi, domin Allah ne kadai zai iya fidda mu daga cikin wannan masifa, domin wannan masifa ce. Kada ka ga ba a taba kayanka ba ko ba a kashe naka ba kai ta murna kana jin dadi, Alhaji mu yi addu’a, Malam mu yi addu’a, Hajiya mu yi addu’a, ubangiji Allah ya kaho mana sauki.
Wassalamu Alaikum…