Ɗan wasan gaban Super Eagles, Sadiq Umar, tare da ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Kaduna Ta Arewa, Hon. Bello El-Rufai, sun kammala sayen ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Rancher Bees FC da ke Kaduna.
Ƙungiyar Rancher Bees za ta shiga gasar NNL a kakar wasa mai zuwa.
- Ba Iya Yunwa Ce Kaɗai Ke Kashe Ƙananan Yara A Katsina Ba – Gwamnati
- Babban Dalilin EFCC Na Yi Wa Tsohon Gwamnan Sokoto, Tambuwal, Tambayoyi
Wannan ƙungiya tana daga cikin tsofaffin ƙungiyoyin mafi daraja a Nijeriya saboda tarihi da nasarori da ta samu a baya.
Ta taɓa samar da fitattun ‘yan wasa da suka wakilci Nijeriya a matakai daban-daban.
Yayin da yake magana game da wannan ciniki, Sadiq Umar ya bayyana farin cikinsa da cewa: “Ni da abokina Hon. Bello muna son dawo da martabar ƙungiyar.
“Na taso ina kallon wasannin Rancher Bees, ƙungiyar da ta samar da ‘yan wasa da suka yi tashe a Nijeriya. Yanzu mu ne masu mamallakinta, abin alfahari ne a gare mu.”
Ya ƙara da cewa: “Burinmu shi ne mu kai ƙungiyar gasar NPFL. Muna godiya ga goyon bayan magoya baya da mutanen Kaduna, kuma za mu yi iya ƙoƙarinmu wajen dawo da farin jinin Rancher Bees a fagen ƙwallon ƙafa.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp