1.4 Sahur shi ne mai rarrabewa tsakanin azumin musulmi da na mazowwa littafi, watau Yahudu da Nasara:
An karɓo hadisi daga Amru ɗan As, Allah ya ƙara yarda a gare shi, ya ce: “Bambancin da yake a tsakanin azuminmu da na mazowwa littafi, shi ne yin sahur “Muslim (#1095) da Abu Dãwud (#2343) da Tirmizi (#708) da Nasã’i (4/149-150) da Ibnu Maja (#1692).
2.0 Mai yin azumi zai iya yin sahur da duk abin da yake halal ne cinsa ko shansa.
An karɓo hadisi daga Jãbir ɗan Abdullahi, Allah ya ƙara yarda a gare su, ya ce; Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Duk wanda ya nufaci yin azumi, to, ya yi sahur da wani abu” Ahmad (#14950, da #15051), da Abu Ya’alã (Musnad 1930, da 2088) da Ibnu Abi Shaiba (Almusannaf #8916) da Ɗabarãni (Mu’ujamul Ausaɗ 4/117). Hadisi ne hasanun ligairihi.
2.1 An fi so a yi shaur da dabino:
An karɓo hadisi daga Abu Huraira Allah ya ƙara yarda a gare shi ya ce: Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Madalla da abin sahur din mumuni dabino “Abu Dãwud (#2345) da Ibnu Hibbãn (#3475) da Baihaƙi (Sunanul Kubrã 4/398 da Sunanus Sugrã 2/109). Salsalar hadisin ingantacciya ce.
2.2 Ana yin sahur ko da ruwa ne:
An karɓo hadisi daga Abu Sa’id Alkudri, Allah ya ƙara yarda a gare shi, ya ce: Manzon Allah (S.A.W) ya ce:” Sahur abinci ne mai albarka, don haka ka da ku bar shi, ko da ruwa ne mutum ya kurba, haƙiƙa Allah yana yabo Mala’iku kuma suna addu’a ga masu yin sahur “Ahmad (#2281, da #11396, da 11086) da Khallãl (Almajãlisu #43) a lafazinsa ya zo da Karin “Ku yi sahur domin sahur yana kara wa mai azumi kuzari (karfi), kuma yana daga cikin sunna, ko da kurɓar makwalwar ruwa ne, yabon Allah ya tabbata a kan ma su yin sahur “Hadisi ne hasanun ligairihi.
An ruwaito hadisi daga Abdullahi ɗan Amru, Allah ya ƙara yarda a gare su, ya ce: Manzon Allah (.SA.W) ya ce: “Ku yi sahur ko da kuwa kurɓur ruwa ne “Ibnu Hibbãn da Abu Nu’aim (Ma’arifatus sahabati (#4191) Hadisi ne sahihi.