Ana so a jirkinta yin sahur zuwa karshen dare. Akwai hadisai da suka nuna haka.
An karɓo hadisi daga Sahlu dan Sa’ad Allah ya kara yarda a gare su, ya ce: “Na kasance ina yin sahur tare da iyalaina, sai na yi gaggawa (zuwa masallaci) domin na riski sallar asuba tare Manzon Allah Sallallahu alaihi wa alihi wa sallam” Bukhari (#577, da #1920)
An wani hadisi daga Anas dan Malik daga Zaidu dan Sabit, Allah ya kara yarda a gare su, ya ce: “Mun yi sahur tare da Annabi Sallallahu alaihi wa alihi wa sallam, sa’an nan ya tashi ya tafi salla. Sai na ce: Mene ne tazarar da take tsakanin yin sahur da kiran salla? Sai ya ce: gwargwadon a karanta aya hamsin (matsakaita)” Bukhari (#576, da #1921) da Muslim (#1097)]
A cikin wannan hadisi akwai halaccin mutum ya fita da dare domin wata bukata, domin Zaidu dan Sabit ba tare da Annabi suke kwana ba, kuma akwai halarcin a taru domin a yi sahur. Domin ganin haka duba Fathul Bãri (4/495)
Amma mai azumi ya kula matuka wajen kirdadon karshen dare. Sannan mutum ya yawaita addu’a da tuba da istigfari da neman gafara, domin lokaci ne na karbar addu’a.