Yin sahur shi ne yake rarrabe azumin Musulmi da na Yahudu da Nasara.
An karÉ“o hadisi daga Amru É—an As Allah Ya Æ™ara yarda a gare su, ya ce: Manzon Allah (S.A.W) ya ce:” Abin da ya rarrabe azumimmu da na Yahudu da Nasara, shi ne cin abincin sahur” Muslim (#1096) da AbÅ« DãwÅ«d (#2343) da Tirmizi (#709) da Nasã’i (Almujtabã 4/150)
Sulaiman al-Khaddabi ya ce :” Ma’anar wannan hadisi shi ne; zaburarwa ce akan yin sahur da shelanta cewa wannan addinin na Musulunci addini ne mai sauÆ™i” Duba; Ma’ãlimu as-Sunan (2/103).
Ma’anar Albarkar Yin Sahur
“Albarka a cikin yin sahur shi ne sakamako da lada ko kuma albarka na karfin da mai azumi zai samu da nishadi idan ya yi sahur, kuma an ce albarka ta kunshi tashin da mutum zai yi da addu’ar da zai lokacin yin sahur, abin da ya fi wajen fassara albarkar yin sahur shi ne, ya kunshi bangarori da dama, yin sahur bin sunna ne, da kuma sabawa Yahudu, da Nasara.
Sahur yana karfafar mutum akan bauta, kuma yana kara nishadi, da kuma tunkude miyagun halaye da yunwa take sawa, kuma yana sa a yi sadaka ga wanda ya yi bara a wannan lokacin ko kuma su hadu da shi su ci, kuma yana sa a yi zikiri da addu’a domin lokaci ne da ake zaton amsar addu’a, da kuma riskar niyya ga wanda ya gafala kafin ya yi barci.
Ibnu Dakikil Iyd ya ce: “Wannan albarkar zai iya yiwuwa ta koma zuwa ga al’amarin lahira, domin tsayar da sunna yana wajabta lada da karuwarsa, kuma zai iya yiwuwa ta koma zuwa ga al’amarin duniya kamar samun karfin jiki wajan azumi da samun saukinsa ba tare da mai azumi ya cutu ba” Duba Fathul Bari [4/496] na Hafiz Ibnu Hajar , bugun darul Fikr.