Manazarci akan harkar tsaro kuma matashin dan siyasa, Salisu Alhassan Dan Sarki ya bayyana cewa, matsalar da Nieriya ke ciki zai yi wahala a magance ta matukar ba a hana cin hanci da rashawa ba.
Ya kara da cewa, “babbar hanyar magance cin hanci da rashawa ita ce, shugabanni su yi gaskiya da adalci”.
- APC Ba Ta Da Ƙarfin Da Za Ta Lashe Zaɓen 2027 Ba Tare Da Kwankwaso Ba – Dungurawa
- Gwamnatin Tarayya Za Ta Ceto Ɗaliban Kebbi Da Aka Sace — Shettima
A cewarsa, nau’in shugabanni hudu ne ke jagorantar al’umma: shugabannin siyasa, da manyan ‘yan kasuwa da sarakunan gargajiya da kuma malaman addinai. Idan waɗannan ɓangarori suka tsaya kan gaskiya to babu shakka za a magance matsalar.
Dan Sarki, ya yi wanan karin hasken ne a wata ganawa da ya yi da wakilin LEADERSHIP Hausa lokacin da yake mika sakon jaje ga hare-haren da aka kai Jihar Kebbi da Kwara, inda ya ce, wajibi sai Nijeriya ta yi amfani da hanyoyi na fasahar zamani domin gano yadda bakin zaren yake kamar yadda sauran kasashen duniya ke yi.
A fannin rashin aikin yi kuwa, Dan Sarki cewa ya yi, hakan ya samo asali ne daga rashin inganta masana’antun cikin gida da gwamnatocin ba sa yi. Inganta masana’antu zai karfafa wa matasa neman aiki don dogaro da kai. Sannan kuma sai gwamnatocin sun ba da himma wajen koyar da sana’o’i da bada jari ga masu kanana da matsakaitan sana’o’i.
Ya ce daga lokacin da aka ce ayyuka da sana’o’i sun wadata to duk ayyukan ta’addanci za su zama tarihi.
Ya jadda bukata shigowar ‘yan majalisun Dattawa da na Wakilai domin taka muhimmiyar rawa wajen samar da zaman lafiya, da yanayi mai kyau ga ‘yan kasa da kuma adalci a kowane ɓangare, yana mai cewa duk dan majalisar da aka zaɓa a matsayin wakilin al’umma kuma ya gaza kare muradunsu to a hankali kima da mutuncin kasar yake zubarwa.














