A jajibirin taro na 32 na shugabannin kasashen kungiyar raya tattalin arzikin yankin Asiya da Pasifik ta APEC, kafar CGTN ta kasar Sin ta gudanar da wani nazarin jin ra’ayin jama’a daga kasashe 15 mambobin kungiyar. Nazarin ya nuna cewa, masu bayyana ra’ayoyinsu sun gamsu da rawar da APEC ke takawa wajen inganta ci gaba a tsakanin kasashen mambobinta, kana sun jinjinawa hangen nesa na kasar Sin da gudunmuwarta ga dunkulewar tattalin arzikin yankin Asiya da Pacific.
Cikin nazarin, kaso 81.9 na wadanda suka bayyana ra’ayinsu sun bayyana goyon bayansu ga shawarar da Sin ta gabatar ta gina al’ummar Asiya da Pasifik mai makoma ta bai daya dake hade da juna, mai bude kofa da samun ci gaba ta hanyar kirkire-kirkire da moriyar juna. Haka kuma, kaso 83.4 sun yaba da gudunmuwar da Sin ke bayarwa wajen daukaka ci gaba mai dorewa a yankin Aisya da Pasifik, da gabatar da dabarunta na ci gaba da dimbin damarmakin kasuwanci ga sauran kasashe, da kuma mara baya ga tsarin gudanar da cinikayya tsakanin bangarori daban-daban, wadanda suka kasance muhimman gudunmuwa 3 da aka bayyana.
CGTN da hadin gwiwar jami’ar Renmin ta Sin ne suka gudanar da nazarin ta hannun cibiyar nazarin dangantakar kasa da kasa a sabon zamani. Mutane 4,048 daga kasashe 15 mambobin kungiyar APEC ne suka bayyana ra’ayoyinsu. (Mai fassara: FMM)













